
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hana rashawa da Laifuka masu kama da ita, ICPC ta kama kantoman ƙaramar hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano, Zangina Galadima Zango.
ICPC ta kama shi ne kan zargin sauya akalar wasu kuɗaɗe da gwamnatin jihar ta yi ta hannun kantomomi 44 na faɗin jihar.
Jin haka ke da wuya, sauran kantomomin ƙananan hukumomin suka arce bayan wani yunƙuri na kamo su da jami’an hukumar suka yi kamar yadda rahotonni suka bayyana.
Hakan ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen labarai, cewa an yi garkuwa da kantomomin ne.
A kwanakin baya ne aka ruwaito cewa, kantomomin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomin jihar 44 tare da kwamishinan ƙananan hukumomin jihar, wanda kuma shi ne Mataimakin gwamnan jihar, aka haramta wa ICPC gudanar da bincike akan su, cin mutuncinsu ko kuma gayyatar ɗaya daga cikin su akan batun.
Kawo yanzu dai ICPC na tsare da Zangina Galadima wanda a ranar Litinin za a gurfanar da shi don amsa tambayoyi kan al’amarin.
