Tuƙa-tuƙar Naira biliyan 1.2 a Sokoto: Tsakanin sani da rashin sani

Spread the love

Daga BILKISU YUSUF ALI KANO

A kwanakin baya Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji (Dakta) Ahmad Aliyu, ya yi wata magana kan haƙa rijiyar burtsate (wato ‘borehole’ a turance), amma adadin kuɗin da ya faɗa sai aka yi masa ca! aka fara yaɗa farfaganda har abin ya zama abin zolaya ga waɗanda suka jahilci mai gwamna yake nufi da abin da gwamna zai yi. 

Faɗin za a yi ‘borehole’ masu ƙaramin sani sai suka ɗauka ‘borehole’ ce irin wanda aka saba yi a gidana da gidanka. Injiniyoyin kirki da yake sana’arsu ce haka ‘borehole’ ka ji sun yi magana? To, ba su ce komai ba, saboda sun san ‘borehole’ kala-kala ce kuma kuɗi–kuɗi ce; ta danganta da ina za a gina ta da wanda zai gina ta da kuma amfanin da za ta yi. Wato waɗanda za su amfana da ita.

Bari na ba ku misali; ‘borehole’ irin ta gidanka da gidana, idan za a yi ta ana haƙa ta ne ko dai a cikin gida ko a waje kuma ta ba wa cikin gida ruwa da ’yan fanfuna a ƙofar gida. Wannan ba za ka haɗa kuɗinta da ‘borehole’ ɗin da za ka yi wanda za ta ba wa unguwa ko gari ruwa ba, musamman garuruwan karkara.

Ana ‘borehole’ ɗin zamani mai aiki da solar  da ‘panel’.  Shi kansa ‘panel’ ɗin ya danganta daga ɗaya har 100. Bayan ‘panel’ akwai manyan tankuna na ƙarfe da ƙarafunan da ake ɗora tankin akai, duka su ma kuɗi ne wanda kai Mista Lay-man ba ya cikin tsarin ‘borehole’ ɗinka mai ƙaramin ƙarfi. 

Daga inda za a yi ‘borehole’ ɗin zuwa inda za a janyo a kai ruwan ka san mita nawa ne? Ba ka da wannan adadin, amma ka ke jayayya akan kuɗin? Ba na mantawa, a Kano a shekarun baya an taɓa irin wannan cece-kucen akan za a yi ‘borehole’ a sakatariyar Audu Baƙo akan kuɗi Naira miliyan 27 a ma wancan lokacin kuma ko a lokacin da aka fito da kuɗin dalla-dalla sai aka ga ma sai an yi ciko, bare a Naira irin ta yau ko Dala irin ta yau. 

Hatta a bututun da za a saka, zurfinsa a ‘borehole’ da ake yi a gida ba ya fin mita 50 zuwa 60 kuma a samu ruwa wanda zai isa buƙatun mutanen gidan. Ba za ka haɗa kuɗinsa da irin wannan ‘borehole’ ɗin da Gwamnan Sakkwato yake bayani ba, wanda za a yi mita ɗari biyu har zuwa ɗari hudu a ƙasa, saboda adadin waɗanda za su amfana da ruwan da iya nisan da ake son a kai ruwan da kuma ƙarko ko ‘ƙuality’ na aikin da ake buƙata ruwan ya kai, don amfanin al’umma.

A dai ɓangaren bututu ɗin dai, shi ma inci-inci ne kaurinsa. Don haka irin wannan bututun ana amfani da inci biyar ne maimakon bututu mai inci ɗaya ko biyu da ake amfani da su a ƙananan borehole.

Kada kuma a  manta, wurin da za a yi irin wannan ‘borehole’ yana da bambanci daga wuri zuwa wuri. Sokoto kowa ya san tana kusa da Sahara. Don haka inda za a haƙa a samu ruwa yana  da bambanci da inda za a yi a Kano ko Jigawa ko Bauchi. Hatta motocin da suke haƙa ‘borehole’ ɗin sun bambanta da wacce ake yi a wasu jihohi da garuruwa.  

Don haka, don an ce za a yi ‘borehole’ kan Naira biliyan 1.2 guda 24 a Sokoto, bai kamata ya zama abin surutu da cece-kuce ba, kamata ya yi a tsaya a ga wanne irin ‘borehole’ za a yi tukunna.

Ya kamata adawar siyasa da ma waɗanda su ba adawar suke ba, fatansu kawai su ga kuskure su yaɗa, ya kamata su jira. Bahaushe yana cewa, “komai gaggawar ungozoma ta jira dai a haihu.”

Don haka Mai Girma Ahmad Aliyu a dai yanzu yana kan aiki bai yi kuskure ba a faɗin za a yi sababbin ‘borehole’ ne da kuɗin kuma za a yi masu inganci ne da nisan zango. Hatta ‘pumping machine’ (injin tunkuɗa ruwa) za a yi amfani da ‘grundfos submersible pump series fiɓe’ ne ‘AC DC‘. Don haka yana da bambanci da wanda ake amfani da shi yau da gobe a gidaje da unguwa.

Da kyakkyawan fatan duk inda matsalar ruwa  take idan dai waɗannan ‘borehole’ sun tabbata to za a yi sallama da matsalar da yardar Allah. Allah ya sa mu dace, amin.

Bilkisu malamar jami’a ce a Jami’ar Alƙalam da ke Katsina kuma marubuciya ce ’yar asalin Jihar Kano

By ukarofi