Daga MUHAMMAD TAJAJJINI DAN TIJJANI
Gaskiya ana yi wa Musulmi ’yan Arewa abin da aka ga dama a ƙasarmu Nijeriya. Yanzu dai kowa yana da labarin auren ’yan mata marayu da aka ƙudiri niyya aka kuma shirya yi a Jihar Neja ranar 24 ga Mayu, 2024, wanda Rt. Hon. Abdulmalik Sarkin-Daji, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, ya ɗauki nauyin gudanarwa.
Sannan kuma kun ji irin taƙaddamar da ta wanzu akan lamarin waccar Ministar Harkokin Mata ta ƙasa, Hon. Uju Kennedy-Ohanenye, ta ƙalubalanta, har ta kai zancen kotu.
Dalilinta, wai auren dole za a yi wa marayun nan. Tambayoyin da zan yi a nan su ne, shin ko ministar nan ba ta shige gona da iri ba kuwa? Ta tuntuɓi Kakaki Majalisa, Sarkin-Daji, don ta ji ya aka yi ake neman haihuwa a ragaya? Shin akwai wata doka ta ƙasa da ta hana iyaye su aurar da ’ya’yansu mata idan sun kai munzalin yin aure? Ko da inda aka haramta wa wani ɗan Najeriya taimakon wasu akan abin da ya dame su muddun abin nan bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa ba? Me zai sa a dinga katsalandan akan harkar da ta shafi addini, al’ada da gargajiyar mutane idan har bai taɓa halaccin abun ba a ƙasa? Ko kuma dai neman suna ne na a san da zamanta tana aiki ko duniya su gan ta a fagen ƙwatar wa mata haƙƙinsu, wato “feminism” ke nan a ɓangaren ministar?
Idan ba haka ai da sai ta nemi masaniya, bayani, ba’asi da dai irinsu kafin ta buɗe baki ta ce ga zance ga magana. Kuma fa abin zai iya zuwa da ƙyashi da baƙin ciki tunda sau da yawa za ka iya samun manyan mata da ba sa fatan alkhairi ga ’yan mata wajen yin aure, don su ma ba su samu sun yi akan lokaci ba? Don haka duk inda suka ga wata za ta yi aure sai sun nemi su hure mata kunne ko ma su hana ta yi gaba ɗaya idan damar hakan ta samu.
Ala ayya halin dai tamu ba irin tasu ba ce. Wai sai daga baya zance ke fitowa cewa, za ta nemi zama da masu ruwa da tsaki, wato malamai, manyan gari, iyayen marayun nan da za a aurar da ma su kansu ‘yan matan wanda wannan ba komai ba ne illa ihu bayan hari.
Wani lokaci na kan tambayi kaina wai ina ƙungiyoyi masu kare haƙƙin bil adama ne? Ina ɗaiɗaikun ‘yan ƙwatar haƙƙin mata ne? Ina fitattu, gogaggun masananmu Musulmi ne? Na dai ji ƙungiyar Lauyoyi Musulmi ta ƙasa (MULAN) ta shiga lamarin, wanda abu ne da ya dace. Hakan sara ne a daidai kan gaɓa.
Gaskiya ya kamata mu dinga yin magana da kakkausar murya game da irin wannan shiga sharo ba shanun da ake yi wa Musulmi ’yan Arewa akan haƙƙoƙinsu wajen gudanar da rayuwarsu a ƙasar nan. Akwai rashin sanin darajar haƙƙinsu na cewa su ma fa ’yan ƙasar nan ne masu cikakken iko kamar kowa. Idan fa muna bari kowa ya bushi iska sai ya zo ya tsoma bakinsa a abin da bai shafe shi ba ko ba shi da ilimi akai, to a ko da yaushe mu ne za mu dinga zama wata al’umma mai kama da irin tabarmar nan ta share kazanta a k’ofar shiga ɗaki.
Amma a kullum da matsayinmu, iliminmu, wayewarmu da ƙololuwar addininmu kuma mu bar kanmu mu zama wulaƙantattu, gafalallu, wofaffu da ba su san ciwon kansu ba su san kishin kai da kare haƙƙinsu ba hakan a gaskiya sam-sam bai dace ba.
Tijjani marubuci ne kuma mai nazarin harkokin yau da kullum mazaunin Kano – Nijeriya. ©️2024
