
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna damuwarsa kan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar da asubahin ranar Lahadi.
Aƙalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu bayan jirgin ya ƙwace a rafin Bakin Kasuwa na gundumar Uban Dawaki da ke ƙaramar hukumar.
Wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamna Lawal ya bayyana hakan a matsayin abin alhini da kuma tausayawa inda ya umarci Hukumar bada agaji ta gaggawa reshen jihar (ZEMA) ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace game da lamarin.
Dauda Lawal ya kuma umarci kwamishinan Ma’aikatar Jin-ƙai da Lamuran Sauƙaƙawa Al’umma ya gaggauta samar da kayan tallafi ga waɗanda hatsarin ya rutsa da su da iyalansu.
