An samu ruɗani bayan EFCC ta ce Yahaya Bello ba ya ofishinta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC ta musanta rahotonnin da ke cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya na wajenta.

A ranar Laraba ne Daraktan Ofishin Labaransa, Ohiare Michael ya ce Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa inda ya ce ya je hedikwatarta tare da wasu manyan ƴan Nijeriya.

Saidai, EFCC, kamar yadda mai magana da yawunta, Dele Oyewale ya faɗa cikin wata takarda, ta ce har yanzu ana neman tsohon gwamnan kasancewar akwai takardar kamu da aka fitar akan sa.

EFCC ta sanar da neman Bello ne ruwa jallo kan zargin badaƙalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 80.2.

By Babaji