Gwamnatin Tarayya za ta garƙame masu zaman kansu da ke biyan ƙasa da sabon mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gargaɗi kamfanoni masu zaman kansu kan ƙin bin dokar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aika wanda yin hakan laifi ne na sata.

Sakataren Ma’aikatar Ƙwadago da Ɗaukar aiki, Alhaji Ismail Abubakar ya faɗi hakan a taron ƙungiyar masu ɗaukar aiki na hukumomi masu zaman kansu a Legas karo na 13.

Alhaji Abubakar, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce duk kamfanin da bai biyan ma’aikatansa mafi ƙaranci N70,000, to za a garƙame shi a kurkuku.

Daraktan ɗaukar aiki da biyan albashi na ma’aikatar, John Nyamali wanda shi ya wakilci sakataren, ya ce mafi ƙarancin albashin doka ce don haka za a hukunta duk wanda aka gano bai biyan kowane ma’aikacinsa da shi.

Ya ce, wajibi ne hukumomi masu zaman kansu su tabbatar duk yarjejeniyar da za a ƙulla tsakanin su da ma’aikansu kar albashin ya gaza mafi ƙarancin albashin, ya na mai cewa hakan na nufin bayan an yi duk rage-rage kamar na haraji da makamantansu.

A lokacin da ya ke magana game da batun, Shugaban ƙungiyar Dakta Olufemi Ogunlowo ya ce akwai buƙatar a fahimtar da su ko N70,000 ɗin ya ƙunshi idan an yi rage-rage ko kuma akasin haka, ya na mai cewa su na ƙoƙari akan hakan tare da samar da ayyuka masu kima ga ƴan Nijeriya da kuma dakatar da duk wasu nau’ukan ɓarnata albarkatun al’umma.

A ranar 29 ga watan Yuli, 2024 ne Shugaba Tinubu ya tabbatar da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Nijeriya daga N30,000 da ake biya a baya.

By Babaji