Shugabanci nagari ba zai yiwu ba idan ɓarayi na mulki – Obasanjo

Spread the love

Tsohon shugaban ƙasan Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa gurɓatattun ‘yan siyasa ba za su iya samar da shugabanci nagari ba, tsohon shugaban ya faɗi haka ne a wani taro na tunawa da Dennis Joseph Slattery a cibiyar Civic Centrer da ke Victoria Island Legas.

Taron wanda ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na St Finbarr ta shirya domin karrama tsohon ɗan ƙasar Ireland Dennis Joseph domin irin gudunmuwar da ya bayar lokacin da ya isa Illewe- Ekiti a Nijeriya shekerar 1941.

A jawabinsa Obasanjo, ya kira gurɓatattun shugabanni a matsayin ɓarayi waɗanda ba za su iya samar da shugabanci nagari ba. Ya kuma jaddada irin lalacewar al’amura a kowanne mataki da gwamnati saboda irin waɗanda ke riƙe da waɗannan waurare.

Ya cigaba da cewa, idan ka kalli ɓangaren zartaswa da na majalisa za mu lura cewa mafi yawa waɗanda ke riƙe dasu sun cancanci a ɗaure su tsawon lokaci da yawa domin irin ayyukan da su ka aikata a baya.

Marigayi Joseph an tura shi makarantar St Gregory da ke Obalende a Jihar Legas 1943 domin ya yi aiki a matsayin mai karantarwa da kuma mai kula da wasanni. Daga nan ya kafa makarantar St Finbarr a watab Janairu 1956. Joseph ya kasance kuma shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya da kuma kafa ƙungiyar ƴan jarida ta Nijeriya (NUJ).

Obasanjo ya karrama shi da lambar girmar Order Of the Niger OON a shekarar 2001.

Joseph ya mutu a watan Yuli shekarar 2003. Taron tunawa da shi ya samu halartar mutane irin su tsohon gwamnan Kuros Riba Donald Duke da tsohon ɗan wasan ƙwallo ƙafa Segun Odegbami

By ukarofi