Shettima ya tafi Amurka don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 79

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bar Abuja don tafiya zuwa ƙasar Amurka domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 (UNGA).

Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha (ta ofishin mataimakin shugaban ƙasa) ya fitar, ya ce Shettima ya tafi taron ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce, Shugaban ya umarci mataimakin nasa ya halarci taron ne don zai mayar da hankali kan al’amuran cikin gida musamman game da annobar ambaliya da ke faruwa a wasu sassan Nijeriya a halin da ake ciki.

A yayin taron, Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya da shiga tattaunawa game da wasu batutuwa na ci-gaba don amfanin Nijeriya da ƴaƴanta.

By Babaji