
Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da aka kammala sati guda da kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ke dakon man fetur daga matatar Ɗangote, mafi yawancin gidajen mai ba su samu man ba.
Ƙungiyar ƴan kasuwar fetur mai zaman kanta ta Ƙasa (IPMAN) wacce ke wakiltar kashi 70 na gidajen man Nijeriya ta bayyana hakan duk da cewa matatar ta fara sayar wa NNPCL.
Shugaban ƙungiyar, Abubakar Maigandi ya ce har yanzu su na jiran samun fetur daga matatar.
A ranar Lahadi da ta gabata ne, NNPCL ya fara dakon fetur daga matatar Ɗangote wacce ke iya fitar da ganga 650,000 a kowacce rana.
A halin da ake ciki, NNPCL ya ce zai ke fitar da lita miliyan 16.8 na fetur wanda ya ci karo da jawabin matatar a farko na cewa lita miliyan 25 za a ke fitarwa.
Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye ya ce motocin ɗibar fetur 70 ne suka fitar wa kamfanin mai a ranar farko.
Saidai, ƴan kasuwa masu zaman kansu zuwa yanzu ba su samu damar sayen fetur daga matatar ba wadda wa NNPCL da rassansa kaɗai ta ke sayar wa.
Sakataren yaɗa Labarai na IPMAN, Cif Okadike Chinede ya tabbatar da cewa mambobisu na cigaba da jiran kira da umarni daga NNPC kan raba musu man.
