Shugaban ƙungiyar “Nigerian Society of Interventional Radiology” Anas Ismail, ya ce Nijeriya na asarar makudan kuɗaɗe wajen fita ƙashen wajen neman lafiya.
Mista Ismail ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Abuja ranar Lahadi a wajen wani liyafar cin abincin dare da aka shirya don rufe taron shekara-shekara na bakwai na ƙungiyar ARIN.
Ya ce asarar ta taso ne sakamakon rashin isassun kayan aikin da likitocin ɗaukar hoton ke yi don gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
“Mahimman ƙalubalen da ke fuskantar aikin ƙungiyar ARIN a Najeriya a halin yanzu suna da alaƙa da rashin isassun kayan aikin da za a yi amfani da su don kula da marasa lafiya da ƙarancin adadin ma’aikatan da aka horar da su don kula da waɗannan marasa lafiya.
“Har ila yau, akwai tsadar wasu kayayyaki, na’urori da kayan masarufi, da ake amfani da su wajen samar da ayyuka. A sakamakon haka, muna rasa adadi mai yawa na marasa lafiya.
Sule Saidu, tsohon shugaban ARIN ya shaida wa NAN cewa likitocin ɗaukar hoto na ba da gudummawa sosai ga kulawar marasa lafiya a asibiti.
A cewarsa, likitocin ɗaukar hoton (radiologists) suna ba da gudummawa ga kulawar marasa lafiya ko dai ta hanyar tantancewa ko shiga tsakani ta hanyar amfani da duban dan tayi, x-ray, da sauransu.
