Badaƙalar N3.1b: Yadda na kai wa Suswam Dala 15.8m a gidansa – Wani shaida ga kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Abubakar Umar, ɗaya ne daga cikin shaidu shida da ke cikin shari’ar tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswan inda ya bayyana wa wata babbar kotu da ke Maitama a Abuja cewa, a shekarar 2014 Suswam a lokacin da ya ke gwamna ya aike shi da Naira biliyan 3.1 don a canja su zuwa Dala.

Kuɗin adadinsa ya kai Dala miliyan 15.8 wanda kuma ya ce ya kai masa gidansa a Maitama bayan an canja su.

Kakakin hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC), Dele Oyewale ya faɗi hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Suswam tare da tsohon Kwamishinan kuɗi, Omodachi Okolobia na fuskantar tuhume-tuhumen kuɗaɗe guda 11 wanda wannan ɗaya ne daga cikin su.

Ba’asi da shaidan ya bayar da bincike da kotun ta yi sun sa an gano cewa tsohon gwamnan ya sa an tura kuɗaɗen ga shaidan don ya yi masa canjin su zuwa Dala inda shaidan ya tabbatar da cewa wata mace ce da ya same su tare ta tura masa kuɗin.

Ya ce, a ranar 12 ga watan Satumba, 2014 aka tura masa miliyan N637 a asusunsa sannan bayan waɗansu mintuna aka sake tura masa miliyan N363.

Sannan a watan Oktoban shekarar an sake tura masa miliyan N630 da ɗoriya a ranar 13 ga wata, sai kuma ranar 17 ga wata inda aka tura masa biliyan N1.06.

Mai Shari’a, Peter Lifu ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga wata Oktoba, 2024 don cigaba da hukunci.

By Babaji