Zargin ta’addanci: Kotu ta amince da ƙarar dake neman tilasta gwamnati ta binciki Matawalle

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata babbar kotu a Abuja ta amince da ƙarar da ke neman a tilasta gwamnati ta yi bincike kan batun zargin alaƙar da ke tsakanin ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle da ayyukan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Wani ɗan gwagwarmayar ƴancin Ɗan-adam kuma mazaunin Zamfara mai suna Abubakar Ɗahru ya shigar da takardar inda ya sanya sunayen Shugaba Bola Tinubu, Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a da Sufeton ƴan sanda a matsayin ƴan ɓangaren amsa ƙarar.

A cikin takardar, Ɗahiru ya nemi kotun ta umarci Shugaba Tinubu ya bai wa Sufeton ƴan sanda umarnin gudanar da bincike game da ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a Zamfara kuma musamman kan zargin Matawalle da hannu a ciki don dawo da zaman lafiya a jihar.

Ɗan gwagwarmayar ya kuma bayyana wa kotun cewa akwai kaso mai tsoka na ayyukan ta’addanci da satar mutane a jihar wanda asali ya fara ne a ƙaramin mataki inda a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2023 ya ta’azzara wanda a lokacin ne Matawalle ke gwamna a jihar.

Har’ilayau ya rubuta cewa, ayyukan ƴan bindiga a jihar ya yi sanadiyyar mayar da dubunnan mutane marayu, zawarawa, gwauraye da rasa gidaje da sabbaba yunwa da sauran ayyukan da ke sanya mutane cikin halin ƙunci.

Kawo yanzu kotun ba ta sanar da ranar da za a yi zama don sauraron ƙarar ba.

By Babaji