Rikicin PDP ya ƙara ta’azzara bayan da Atiku ya goyi bayan tsige Damagum

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya goyi bayan shirin tsige muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum.

Bayanai sun nuna cewa Atiku ya fara tuntuɓar ‘yan kwamitin gudanarwa (NWC) waɗanda suka fara fafutukar sauke Damagum daga shugabancin jam’iyyar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa shirin tsige Umar Damagum ya raba kawunan gwamnoni 13 na jam’iyyar adawa PDP.

Gwamnoni bakwai ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi sun haɗa kai, sun matsala lamba kan dole Damgum ya bar muƙaminsa.

Yayin da gwamnoni huɗu ƙarƙashin Gwamna Seyi Makinde na Oyo suka nuna gamsuwa da Damagum, sauran gwamnoni biyu kuma sun ce duk inda ta faɗi sha ne, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Gwamnonin da suke goyon bayan Damagum ya ci gaba da shugabancin PDP bakinsu ɗaya da Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda alaƙarsa ta yi tsami da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar.

Atiku da Wike dai sun raba gari gabanin babban zaɓen 2023, inda Wike ya jagoranci gwamnoni biyar na PDP wajen yaƙar takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Atiku ya fara tuntuɓar ‘yan kwamitin NWC

Wani babba a NWC, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin magana da ‘yan jarida, ya tabbatar da cewa Atiku ya tuntuɓi wasu daga cikin masu shirin sauke Damagum.

“Ba mu kaɗai ba ne, manyan shugabanni a jam’iyyar da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar sun tuntuɓi wasu daga cikin mu.”

“Ina tabbatar maku da cewa Atiku ya kira wasu daga cikinmu, ya nuna mana ba mu kaɗai za mu yi yaƙin ba, kuma yana goyon bayan neman adalci, gaskiya, da daidaito.

“Ba mu da wata matsala da Damagum, burinmu shi ne mu kare jam’iyyar domin ‘yan Nijeriya su samu mafita a zaɓe mai zuwa. Ya kamata Damagum ya mutunta dokar jam’iyya, ya sauka daga muƙamin.” 

Tun bayan karɓar muƙamin muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa bayan tsige Iyorchia Ayu, masu ruwa da tsaki sun caccaki Damagum kan rashin aiwatar da muhimman sauye-sauye domin farfaɗo da jam’iyyar.

Hankali ya ta’azzara ne lokacin da Kwamitin Ayyukana na ƙasa ya miƙa ragamar mulkin jam’iyyar PDP na jihar Ribas zuwa Wike maimakon Gwamna Siminalayi Fubara. Wannan matakin ya harzuƙa ƙungiyar Gwamnonin PDP, inda suka dage cewa gwamnan jihar yana da ‘yancin zama shugaban jam’iyyar a jihar.

Da aka tambayi majiyar ko me Atiku ya sanar da ‘yan Kwamitin NWC da ke adawa da Damagum, majiyar ta bayyana cewa, “Zan iya tabbatar da cewa Atiku ya yi magana da wasunmu. Ya tabbatar mana da cewa ba mu kaɗai ba ne, kuma yana goyon bayan neman adalci, gaskiya, da daidaito.

Ya ƙarfafa mu mu ci gaba da ƙwazo kuma mu ci gaba da ba da shawarar a bi Kundin Tsarin Mulki na PDP a cikin shawarwarin yau da kullum na NWC. Ya fahimci dalilanmu na son a cire Damagum kuma bai yarda ba.

“Ba mu da wata matsala ta kanmu da Damagum; Burin mu shi ne mu kare jam’iyyar domin ‘yan Nijeriya su samu mafita a zaɓe mai zuwa. Damagum ya kamata ya mutunta kundin tsarin mulki da al’adun jam’iyyar, ya koma kan aikinsa na farko na Mataimakin Shugaban ƙasa (Arewa), kuma ya bar yankin Arewa ta Tsakiya ya zaɓi wanda zai maye gurbinsa cikin gaggawa.”

Wata majiya mai tushe da ke kusa da Atiku ta nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana son a maye gurbin Damagum kamar yadda kundin tsarin mulkin PDP ya tanada. Wannan majiyar ta ce, “Atiku yana haɗa kai da mambobin NWC da sauran jagororin jam’iyyar da suka sadaukar domin ganin an ɗauki matakan da suka dace na mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar.”

Dangane da ko Atiku yana son a cire Damagum, majiyar ta bayyana cewa, “Ba batun Damagum ba ne; tsohon mataimakin shugaban kasar ya mayar da hankali ne kan dimokuradiyya da jam’iyyar PDP. Atiku ya gwammace ya yi aiki da hankali don gyara abin da ya lalace.”

Duk ƙoƙarin jin ta bakin mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, domin jin ta bakinsa ya ci tura, domin bai amsa kira ko amsa saƙonni ba.

Sai dai wani ɗan jam’iyyar PDP na NEC kuma mataimakin shugaban matasa na ƙasa, Timothy Osadolor, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su ƙaurace wa faɗace-faɗace, sannan su miƙa komai ga kwamitocin da suka dace.

A wata tattaunawa ta musamman da wannan jarida, Osadolor ya bayyana amincewa da kwamitocin sulhu da ladabtarwa, inda ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su bar su su yi aiki tuƙuru ba tare da wata tangarɗa ba.

A ranar 21 ga watan Agusta, jam’iyyar PDP NWC ta kafa kwamitoci guda biyu: ɗaya ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan harkokin waje Tom Ikimi kan harkokin ladabtarwa da kuma wani ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Osun Prince Olagunsoye Oyinlola domin sulhuntawa. Kwamitin na Oyinlola yana da alhakin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da magance matsaloli daban-daban, yayin da kwamitin Ikimi zai sake duba koke-koke tare da ba da shawarar sanya takunkumi ga mambobin da suka saba wa dokokin jam’iyyar.

Osadolor ya bayyana cewa, Kwamitin Zartarwa ta ƙasa ta amince da kafa kwamitocin sulhu da ladabtarwa. An ƙaddamar da wadannan kwamitocin kuma a halin yanzu suna aiki. Na san cewa komai bai dace da jam’iyyar ba, amma ina da imani da kwamitin Ilimi da kwamitin sulhu.

“Mambobin da ke da al’amura na gaskiya su tuntubi wadannan kwamitocin su guji ayyukan da za su iya dauke musu hankali. Dole ne mu guji kai hari ga jama’a kuma mu kyale kwamitocin su yi aikinsu,” inji shi.

By ukarofi