Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Libya na ci gaba da bayar da man fetur mafi arha a Afirka, inda farashin lita ya tashi a kan dala 0.032, kwatankwacin Naira 52 na kuɗin Nijeriya.
Wani rahoto da shafin da ke bin diddigin farashin fetur a duniya ya fitar na nuna cewa Libya ce aasar da tafi kowacce arhan man a Nahiyar Afirka.
Idan aka kwatanta, farashin man fetur a Masar, Aljeriya, da Angola ya tsaya kan dala 0.279, dala 0.342, da kuma dala 0.351 kan kowace lita.
ƙasashe huɗu ne kawai a Afirka ke sayar da mai a farashi mai rahusa fiye da Nijeriya.
Alƙaluman da aka samu a yanzu sun nuna cewa farashin man fetur a Nijeriya ya kai Naira 1,000 kan kowace lita, inda farashin man a kasuwar bayan fage ya tashi zuwa Naira 1,600 kan kowace lita.
A halin da ake ciki, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ce ta fi kowacce tsadar farashin man fetur a nahiyar, kan dala 1.83 kan kowace lita.
Senegal (dala 1.646), Seychelles (dala 1.595), Zimbabwe (dala 1.590), Morocco (dala 1.527), da Uganda (dala 1.475) wasu kasashe ne da farashin mai tsada a kowace lita, yayin da Malawi (dala 1.458), Cote d’Ivoire (dala 1.455), Kenya (dala 1.453), da Saliyo (dala 1.448) sun tattara jerin sunayen.
Duk da kasancewar Nijeriya ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke haƙo mai a Afirka, Nijeriya na fuskantar suka kan tsadar man fetur.
Hakan dai ya janyo kiraye-kirayen gwamnati ta tsoma baki a harkar man fetur, inda da dama ke cewa cire tallafin man fetur ya yi illa ga ’yan ƙasar.
