An ɓarke da zanga-zangar matsin rayuwa a Ghana

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

‘Yan sandan Ghana sun ce sun kama masu zanga-zanga 42 a Accra babban birnin aasar, bayan da rikici ya ɓarke a lokacin zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki da yadda gwamnati ke tafiyar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Tun a ranar Juma’a ne aka fara gudanar da zanga-zangar wadda ƙungiyar ‘Democracy Hub’ ta shirya kuma za ta ci gaba har zuwa ranar Litinin.

Masu zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne, sun zagaya cikin birnin suna rera waƙoain kishin ƙasa ɗauke da allunan da ke nuna ɓacin ransu game da lalata muhalli sakamakon haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma yadda gwamnati ke ƙara taɓarɓara tattalin arzikinƙasar.

An kama mutane 42 ne a ranar Lahadin da ta gabata, inji wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar.

“Waɗannan mutane sun taru ba bisa ƙa’ida ba, suka kai farmaki kan jami’an ‘yan sanda da ke gudanar da ayyukansu na doka,” inji kakakin ‘yan sanda Grace Ansah-Akrofi ga AFP.

“Za a gurfanar da su a gaban kotu saboda laifukan da suka aikata, da suka haɗa da hana ababen hawa wucewa, ɓarnatar da dukiya da kawo hargitsi.”

A cikin sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce, masu zanga-zangar sun aikata ta’addanci daban-daban da suka haɗa ƙona motocin ‘yan sanda tare da jefar jami’an, tare da ture shingayen kiyaye haɗarra da kuma kawo cikas ga zaman lafiya.

Sun kuma sanar da farautar wasu jagororin zanga-zangar da suka haɗa da fitaccen lauya kuma mai fafutuka Oliɓer Barker-ɓormawor bisa zargin tsarewa.

Ansah-Akrofi ya ƙara da cewa “Muna aiki don gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a gaban shari’a.”

By ukarofi