Tirela ta kashe duka ƴan gida ɗaya a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani mummunan hatsari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida ƴan gida ɗaya bayan tirela ta take su a yankin Gusau Hotel da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Lamarin ya auku ne a lokacin da iyalan ke tafiya akan babur inda tirelar ta buge su wanda a sakamakon haka, nan take suka mutu.

Mutanen sune Abdurra’uf da aka fi sani da Taye da matarsa Mujjidat da kuma ƴaƴansu guda huɗu waɗanda babu ɗaya daga cikin su da ya rayu.

Al’amarin ya sanya al’ummar yankin cikin alhini tare da jimami kasancewar ahalin sananne ne wanda hakan ya sa aka yi ta addu’o’in alkhairi a gare su.

Hukumomi na gudanar da bincike kan lamarin da ƙoƙarin gano musabbabin aukuwar sa tare da hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.

Haka kuma, lamarin ya nuna yadda hukumar kiyaye haɗurra ke da muhimmanci a cikin al’umma da kuma ƙara kulawa da yankunan da ke fama da cinkoson ababen hawa.

By Babaji