An buƙaci gwamnatin Katsina ta hanzarta gyara Asibitin Ɓaure

Spread the love
Hon. Surajo Umar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin jihar da gaggawa gyara babban asibitin garin Ɓaure da ke ƙaramar hukumar Ɓaure.

Al’ummar garuruwan da ke maƙwabtaka da garin kan je asibitin neman magani.

Ɗan Majalisar mai wakiltar Ɓaure, Hon. Saraki Umar ne ya gabatar da buƙatar haka a zauren majalisar inda ya ce asibitin na fama da rashin isasshen wutar lantarki da sabbin na’urorin kiwon lafiya tare da gyaran gine-ginen asibitin.

Haka kuma, ya ce akwai matsalar ƙwararrun malaman kiwon lafiya da haka ya sa wata lalurar, kamar ta haihuwa da gwaji sai an je asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Daura.

Kakakin majalisar, Alhaji Nasiru Yahaya wanda ya jagoranci zaman, ya ce lallai asibitin garin Ɓaure na neman kulawar gwamnatin jihar cikin gaggawa don rage wa marasa lafiya matsalar zuwa Daura neman magani.

Majalisar dokokin dai ta aikawa gwamnati da buƙatar domin amincewa da kuma yin kwaskwarima da sauran su a asibitin.

By Babaji