

Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Lahadi ne gwamnatin tarayya ta bayar da motoci 64 da ke amfani da iskar gas (CNG) ga Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) da Ƙungiyar Kasuwanci ta TUC da kuma Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS).
An gudanar da haka ne a wajen taro na Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja wanda ya zama ɗaya daga cikin ababen bikin murnar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai.
Ministan Kuɗi da shirin Tattali, Mista Wale Edun shi ya jagoranci tawagar ministoci da suka haɗa da; Ministan Labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris; Ministan Kasafi da tsare-tsaren Tattali, Abubakar Bagudu da kuma ƙaramin Ministan Ci-gaban Matasa, Mista Ayodele Olawande.
A lokacin da ya ke magana, Mista Wale Edun ya ce, raba motocin ɗaya ne daga cikin alƙawuran da shugaba Bola Tinubu ya yi na samar da sauƙi da kuma isasshen ababen sufuri ga al’umma bayan cire tallafin man fetur a ƙarƙashin shirin gwamnatin a ɓangaren harkar iskar gas (PCNGi).
Ya ce, shirin zai taimaka wajen sauƙaƙe wa al’umma musamman marasa ƙarfi kan daidaita al’amuran tattali da zai tafi a yadda ƙasar ta ke gudana.
Ya ƙara da cewa, asalin shirin shine don a raba sama da motocin CNG 500 da kuma na wuta guda 100 a karon fari inda waɗanda da aka bayar sune na sahun farko.
Har’ilayau, samar da motocin na CNG za su taimaka wajen rage kuɗin sayan fetur inda a madadin kashe N50,000 ko sama da haka don cika tanki, yanzu N15,000 ta wadatar.
Sakataren TUC, Kwamared Nuhu Toro ya yaba wa Shugaba Tinubu ga ƙoƙarin nasa da kuma amincewa da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Najeriya.
Haka ma, Shugaban NANS, Kwamared Emonefe ya jinjina wa gwamnatin kan ƙoƙarinta ga harkar ilimi da kula da ɗalibai inda ya bada misali da tsarin bada aron kuɗi gare su da aka samar.
