Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu da yi garkuwa da 40 a Maradun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani mummunan hari da ƴan bindiga suka kai a ranar Asabar da dare, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da yin garkuwa da wasu 40 a yankin Janbaƙo da ke ƙaramar hukumar Maradun na Jihar Zamfara.

Janbaƙo shi ne ƙauyen ƙaramin Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Mazauna yankin sun ce mafi yawancin waɗanda aka sace mata ne da ƙananan yara.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan sako wasu mutane goma da ke hannun ƴan bindiga da aka bai wa miliyan N10 a matsayin kuɗin fansa.

Ibrahim Haru, ɗaya ne daga cikin mazauna yankin wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, ƴan bindigar sun yi ta harbe-harbe a lokacin da suka shiga ƙauyen.

Ya ce, wani mutum mai suna Malam Isa da wani yaro ne aka kashe a lokacin da su ke ƙoƙarin guduwa da ake harbe-harben.

Duk da cewa akwai jami’an tsaro a yankin, hakan bai hana ƴan ta’addar kai harin ba wanda ke ƙara nuna yadda rashin tsaro ke ta’azzara a yankin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya bayyana wa manema labarai cewa, ba su kai ga samun labarin aukuwar lamarin ba a lokacin da ake haɗa rahoton.

By Babaji