Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Kula da Ruwa ta Nujeriya (NIHSA) ta nuna damuwarta kan yadda ruwan ya yi nawa a gaɓar kogin Benuwai, inda ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a yankin nan ba da jimawa ba.
Bayanan da hukumar ta fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, ya nuna yadda ruwa ke ƙaruwa, inda ake daf da fuskantar ambaliyar ruwa.
“Matsalar ƙaruwar ruwa da aka gani a manyan wuraren na da ban tsoro, inda Wuro Boki ke da mita 6.36 da gadar Jimeta a mita 5.04.
“Tashar Ibbi tana da mita 8.2, Makurdi a mita 9.4, da Lokoja (Kogin Neja) mai tsawon mita 8.68,” inji rahoton.
An yi nuni da cewa, ruwan da ke ƙaruwa, musamman a Makurdi da Ibbi, ya sanya kogin Benuwai cikin shirin ambaliya.
Hukumar ta ba da shawarar ɗaukar matakan kariya cikin gaggawa a jihohin da ke kusa da kogin, musamman waɗanda a baya aka gano suna fama da ambaliyar ruwa.
“Tsarin ruwa a muhimmin tashoshin mu da ke gefen Kogin Benuwai har zuwa ranar Asabar, 21 ga Satumba, 2024, na nuna ci gaba da samun ƙaruwar ambaliyar ruwa,” inji NIHSA.
Hukumar ta jaddada muhimmancin inganta wuraren wucewar ruwa da kuma shawo kan ambaliyar ruwa don kare al’umma masu rauni.
Ta ƙara da cewa, za ta sanya ido kan matakan kogin tare da samar da bayanai don taimakawa hukumomi da jama’a don rage haɗarin ambaliya.
NAN ta ruwaito Femi Bejide, Darakta, Operational Hydrology, NIHSA, yana kira ga mazauna yankin da su fice daga wuraren nan da nan.
“Ambaliya da muke gani a yanzu yana faruwa ne sakamakon yawan ruwan sama da ake lafkaw. Duk da haka, ana daf da fara ambaliya a kusa da kogi, kuma zai yi tsanani.
“Al’ummomi a jihohin Bayelsa da Jigawa na fama da rauni saboda yanayinsu. Hukumomi sun ba da shawarar hana yin gine-gine a filayen ambaliyar ruwa, amma duk da haka wannan lamari ne mai sarƙaƙiya.
Bejide ya ƙara da cewa “Mun sha gaya wa mutane su tashi daga waɗannan yankuna, amma matsalar ta tura.”
Daraktan ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya da dama na jiran tallafin gwamnati, wanda ya zama siyasa, abin da ke ƙara dagula ƙoƙarin daƙile wannan lamari.
