
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Mai Shari’a Kudirat Olatokunbo Motonmori da aka fi sani da Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ta 23 a ranar 30 ga watan Satumba, 2024, a majalisar lauyoyi da ke Fadar shugaban ƙasa a Abuja.
An haifi Kekere-Ekun ne a ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 1958 a Landan, a ƙasar Birtaniya.
Ta yi karatun Shari’a a Jami’ar Legas inda ta samu digirin farko a shekarar 1980 wanda bayan kammala karatun makarantar shari’a ne, sai aka tabbatar da ita a matsayin lauya a ranar 10 ga watan Yuli na shekarar 1981.
Ta kuma yi digiri na biyu akan shari’a hallau a makarantar ‘London School of Economics’ da ke Landan wanda ta kammala a Nuwamban 1983.
An kuma bata muƙami a Kotun Ɗaukaka ƙara a shekarar 2004 saboda gudunmawa da take bayarwa a ɓangaren harkar ci-gaban shari’ar a Nijeriya.
A Yulin shekarar 2013 ne aka ƙara mata matsayi zuwa Mai Shari’a ta Kotun Ƙoli.
