
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta naɗa kwamitin bincike game da batun zargin rashawa da saɓa wa ƙa’idodin aiki a Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCos).
Ministan Harkokin Cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Litinin a Abuja inda ya ce kwamitin zai yi bincike game da zargin jami’an hukumar da bai wa Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky mafaka.
Ministan ya ce, akwai buƙatar a tsaftace hukumar don tabbatar da gaskiya da adalci.
A kwanakin baya ne ministan wanda shine shugaban hukumar haɗaka ta hukumomin Civil Defence, gyaran hali da shige-da-fice (CDCFIB), ya dakatar da jami’ai kan saɓa wa dokokin aiki.
Ya kuma yi kira ga kwamitin su tabbatar da adalci ba tare da nuna sassauci ga kowane ɓangare ba.
