Rundunar sojan sama ta Nijeriya ta bayyana gagarumin nasara a yaƙi da ake da ‘yan bindiga a lokacin da ta tarwatsa wani sansanin ‘yan bindigan a dajin yadi da ke ƙaramar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Sanarwar ta fito daga mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Group Kyaftin Kabiru Ali a ranar Litinin a Abuja.
Ali ya bayyana cewa an samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’addan na ɓoye makamai a dajin Yadi.
Bayanan kuma sun nuna cewa makaman mallakar Kadade Gurgu ne, wanda makusanci ne na Dogo Giɗe.
Bayanan sun cigaba da bayyana cewa Kadade Gurgu ya kasance mai ba ‘yan bindiga mafaka daga jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.
