Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta dakatar da shaharren ɗan wasan ƙwallon kafa Samuel Eto’o saboda karya dokokin ta a gasar Kofin Duniya na ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 da aka gudanar kwanan nan.
An zargi Eto’o da karya dokokin a gasar Kofin Duniya na ‘yan mata ƙasa da shekaru 20 yayin wasan da aka yi tsakanin ƙasashen Kamaru da Brazil. An dakatar da shi na tsawon watanni shida tare da hukunta shi saboda karya dokokin da suka shafi halayya da ɗa’a.
Kwamitin Ladabtarwa na FIFA ya fitar da wata sanarwa da ke cewa: “Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya hukunta shugaban hukumar ƙwallon Ƙafa ta Kamaru Samuel Eto’o, da dakatarwa na tsawon watanni shida daga halartar wasannin ƙungiyoyin ƙasar Kamaru saboda karya dokokin sashe na 13 da 14 (Rashin ladabi na ƴan wasa da jami’ai) na dokar ladabtarwa ta FIFA.
“Hukuncin ya shafi wasan zagaye na 16 na Kofin duniya na ‘yan mata ƙasa da shekaru 20 da aka buga tsakanin Brazil da Kamaru a Bogotá, Colombia, a ranar 11 ga Satumba 2024.
Dakatarwar da aka yi wa Mista Eto’o ta hana shi halartar dukkan wasannin maza da mata da suka shafi ƙungiyoyin FECAFOOT na dukkan matakai da rukuni na shekaru. An sanar da Eto’o a yau, ranar da hukuncin ya fara aiki.
