Shahararren ɗan wasan ƙwallon kwando mai tsaron baya, da ya yi fice a gasar NBA ta ƙasar Amurka Dikembe Mutombo ɗan ƙasar Congo ya mutu yana da shekaru 58.
Fitaccen ɗan wasan ya mutu ne bayan fama da cutar sankara a ƙwaƙwalwarsa.
Mutombo wanda ya shafe shekaru 18 yana haskawa a gasar ƙwallon kwandon Amurka, ya lashe kofunan gasar 8, sannan kuma ya kasance daga cikin masu tsaron baya mafi ƙwarewa da ƙwazo a tarihin gasar.
Daga cikin abinda za a riƙa tunawa da Dikembe Mutumbo, akwai gidauniyar ƙashin kansa da ya kafa wadda ya zuba miliyoyin dalar Amurka daga aljihunsa domin taimakawa marasa ƙarfi a ƙasarsa wato Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, inda ya gina wani katafaren Asibiti a ɗaya daga cikin yankunan birnin Kinshasa.
Baya ga ƙasarsa, Mutumbo ya bayar da tallafi a fannoni da dama domin taimaka wa marasa ƙarfi a wasu sassan na Afrika, abinda ya sa shi samun lambobin yabo a ciki da wajen nahiyar, ciki har da kyauta ta musamman daga fadar gwamnatin Amurka saboda jajircewarsa wajen ayyukan jinƙai, duk da cewar a lokaci guda yana ɗauke da nauyin zama Jakadan gasar ƙwallon kwandon Amurka na duniya.
