Cibiyar gudanarwa ta Amurka ta bai wa Gwamna Abba lambar yabo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu kyautar girmamawa daga cibiyar gudanarwa da shugabanci ta ƙasar Amurka.

Kamar yadda wata sanarwa daga kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta bayyana, cibiyar ta bai wa gwamnan lambar girman ne saboda ƙoƙarinsa na samar da cigaba wa al’umma da kula da dukiyarsu.

Wakilin cibiyar, Barista Steven Lounge ya gabatar da hakan a wani taron karramawa, a masauƙin gwamnatin jihar Kano da ke Abuja.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan gwamnan ya samu lambar girma na Ƙasa daga ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) a lokacin zagoryar ranar malamai ta duniya.

Dakta Lounge ya ce, sun yi hakan ne bayan dogon bincike da nazari da suka yi game da ƙoƙarin Abba a ɓangaren kula da al’umma da dukiyarsu.

Binciken nasu ya nuna yadda gwamnan ke ƙoƙari wajen inganta shugabanci na gari a Kano wadda ita ce jiha mafi yawan al’umma a Nijeriya, ya na mai cewa suna alfahari da haɗa hannu da ire-iren sa.

A lokacin da ya ke magana, Gwamna Abba ya bayyana godiyarsa gare ta ganin yadda aka yaba da aikinsa a mataki na ƙasa-da-ƙasa inda ya kuma tabbatar da cewa za su cigaba da aiki tuƙuru wajen raba wa al’umma romon demokraɗiyya.

By Babaji