Jirgin Emirates ya sauka a Legas karon farko cikin shekara biyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A karon farko cikin shekaru biyu, jirgin Emirates ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas a ranar Talata.

Jiragen yankin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) sun koma aiki bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a shekarar 2021 saboda matsalolin da ba a warware ba, ciki har da maƙalewar kuɗaɗen kamfanin a Nijeriya.

Jirgin EK 783, Boeing 777-300ER, ya sauka a tsohuwar tashar MMIA da ƙarfe 3:32 na yamma. Haka zalika, jirgin ya isa tare da kujeru da yawa da babu kowa, wanda ke nuna gazawar komawa aiki.

Yayin da ba a iya tabbatar da adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba, fasinjojin da suka zanta da manema labarai sun ruwaito cewa jirgin bai cika ba.

“Jirgin bai cika ko kaɗan ba amma kamar yadda aka saba, ayyukan sun yi kyau sosai. Kuma ina ganin wannan abu ne mai wuyar fahimta kasancewar jirgin na farko bayan shekaru da yawa,” inji wani fasinja.

A cewar jami’an filin jirgin, an sarrafa fasinjojin da suka tashi ta hanyar sabuwar tashar da aka bude, yayin da waɗanda suka isa filin jirgin suka nufi Old Terminal.

Jirgin Boeing 777-300ER yana da fasinja 392, amma karancin matafiya da ke cikin jirgin ya nuna cewa komawar kamfanin zuwa kasuwannin Nijeriya zai ɗauki wani lokaci kafin ya farfaɗo bayan tsawaita hutun.

Duk da haka, sake dawowa ya nuna wani muhimmin mataki na maido da cikakken ayyukan ƙasa da ƙasa a MMIA.