A ranar Alhamis ne Rafeal Nadal ya sanar da cewar zai yi ritaya daga wasan ƙwallon Tennis bayan kammala wasan ƙarshe na gasar kofin Davis, inda zai kawo ƙarshen sana’ar da ta ba shi damar samun kambun Grand Slam sau 22.
“Zan yi ritaya daga wasan ƙwallon Tennis. A zahiri al’amura sun yi tsanani a ’yan shekarun baya-bayan nan, musammanmma shekaru 2 da suka gabata,” inji Nadal a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta.
“Haƙiƙa wannan shawara ce mai wahalar yankewa, wacce ke daukar tsawon lokaci kafin a yanke. saidai a rayuwa duk abinda ya yi farko ta zai yi ƙarshe.”
An haɗa Nadal da Carlos Alcaraz a cikin tawagar ƙasar Sifaniya a yayin da yake ƙoƙarin karkare kawo ƙarshen sana’ar tasa da samun nasara a gasar kofin Daɓis karo na 5 da za ta gudana a Malaga a wata mai kamawa.
Nadal ya samu mutunci a idon duniya tare da zama gwarzon da ake koyi da shi, da kuma yin gogayya da zaratan ’yan wasan Tennis irin su Roger Federer da Novak Djokovic.
