‘Yan Majalisa sun nemi a yi gaggawar janye ƙarin kuɗin fetur da gas

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Majalisar Wakilai ta fara duba batun ƙarin farashin man fetur da gas a ƙasar nan.

Wannan ya biyo bayan ƙudurin da Aliyu Madaki ya gabatar, tare da goyon bayan mambobi 111 na majalisar, inda suka buƙaci a gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da gas ɗin girki.

‘Yan majalisar sun bayyana damuwarsu cewa ƙarin farashin yana jefa ‘yan Nijeriya cikin ƙunci, tare da barazanar rashin aikin yi.

Haka kuma, Majalisar ta nemi Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) da ma’aikatar albarkatun man fetur su ƙara ƙarfin tace man fetur a cikin gida, tare da yin kira ga babban bankin Nijeriya ya aiwatar da manufofin kuɗi da za su rage illolin da ƙarin farashin mai zai haifar ga hauhawar farashi a ƙasa.

A gefe guda kuma, Babban Bankin Duniya ya gargaɗi cewa ƙarin farashin man fetur zai iya janye tasirin cire tallafin mai da aka fara gani a Najeriya.

Wannan gargaɗi yana ƙunshe ne a cikin rahoton Africa’s Pulse na watan Oktoba na Bankin Duniya.

By ukarofi