
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta bada sabon umarni game da wasan neman gurbin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka ta 2025 tsakanin Libiya da Nijeriya.
A baya ne dai aka bar tawagar Super Eagles a wulaƙance a lokacin da suka je ƙasar Libiya don buga wasan ba tare da marabtar su irin yadda ake yi wa baƙi ba.
A ranar Talata ne CAF ta sanar da cewa, ba za a buga wasan ba kamar yadda aka tsara shi inda tace za ta miƙa lamarin ga ofisoshin ƙwararru na hukumar don ji da lamarin.
Tun da farko dai, CAF ta yi watsi da irin yadda aka mu’amalanci Super Eagles ɗin a ɗaya daga cikin Filin jirgin sama na ƙasar ta Libiya, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.
