Yanzu-yanzu: Jagororin NLC da TUC na ganawa da Gwamnatin Tarayya kan tashin farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jagororin ƙungiyoyin ƙwadago da na kasuwanci (NLC da TUC) na ganawa da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin sakataren gwamnatin kan sabon ƙarin da aka yi wa litar fetur a Nijeriya.

Ana gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Sakataren gwamnatin ƙasar, Sanata George Akume wanda musamman don ƙalubalen da hakan ke yi ga al’ummar ƙasa aka shirya shi.

Cikin mahalarta zaman akwai; Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu da Ministan Tattali, Wale Edun da kuma Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha.

Sauran sun haɗa da; Ministan Labarai, Mohammed Idris da ƙaramin Ministan Man fetur, Heineken Lokpobiri da wasu wakilai daga kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL.

By Babaji