Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
A ranar 7 ga watan Oktobar nan a ke cika shekara daya da fara arangamar da a ke ciki a yanzu tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa ko a ce kai tsaye ƙungiyar mayaƙan Hamas da ke mulkin Gaza. Haƙiƙa Hamas ba ta yi zaman tunawa da cika shekara daya da fara wannan yaƙi ba kamar yadda Isra’ila ke duba lamuran da su ka faru a tsawon wata 12.
Yayin da Hamas ke aiki da rokoki da ta ke jefawa ko ma aiki da wuƙaƙe da duwatsu da sauran su, Isra’ila na amfani da jiragen yaƙi ne da na’urorin da duk duniya aka iya bayyana su a matsayin mafiya inganci wajen yaƙin zamani. Kai tsaye akwai ƙasashe da ke mara baya ga Isra’ila don yin galaba a wannan yaƙi. A bangaren Hamas wacce ba ta shafi dukkan ƙasar Falasɗinawa ba wato kamar wata jiha ce a ƙasar Falasɗinu, na samun tausayawa ne daga wasu ƙasashe ko goyon baya daga ƙungiyoyin da su ka haɗa da Hezbollah a Lebanon da Houthi a Yaman.
Bambancin a fili ya ke yayin da Isra’ila ke yaƙi a matsayin ƙasa da ke tinƙaho da mallakar zaratan makamai da goyon baya daga yammacin duniya, Hamas na yaƙi ne kusan na sunkuru daga ramukan ƙarƙashin ƙasa da zummar tabbatar da samuwar ’yancin ƙasar Falasɗinawa. A kan kai agajin makamai kai tsaye ga Isra’ila duk da ta na da makamai masu zunzurutun yawa da inganci ga hukumar leƙen asiri da ke ɗaukar kan ta a sahun farko a duniya wato MOSSAD da ke jera kan ta a layi ɗaya ko ma ta sha gaban hukumar CIA ta Amurka da KGB ta Rasha.
Su kuwa ƙungiyoyin da ke mara baya ga Hamas ba sa iya shigowa yankin Gaza sai dais u tsaya daga inda su ke su na nuna turjiya kamar Houthi da kan yi amfani da hare-hare ta tekun Bahar Maliya ga jiragen ruwan ƙasashen da ke mara baya ga Isra’ila. Su kuma ƙasashen kan maida martani wajen ’yan hare-hare ga sassan da ke ƙarƙashin Houthi a Yaman ta hanyar da ba sha’awar wargaza Houthi don ita ma akwai muradun da a kaikaice ta ke karewa ƙasashen da ke marawa Isra’ila baya. Har yau waɗannan ƙasashen ba su amince da ayyana Houthi a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba.
Hezbollah kuma na amfani da tsohon yaƙin ta na kan iyakar Lebanon da Isra’ila. Hezbollah ta daɗe ta na arangama da Isra’ila amma na wannan karo ya yi tsanani da Isra’ila kan auna jagororin Hezbollah don kawar da su da zummar karya lagon Hezbollah din. Can ma a Sham akwai mayakan Hezbollah da wasu kwamandojin yaki daga Iran da kan yi aiki don kare gwamnatin shugaba Bashar Al’Asad na Sham ɗin da Iran ke marawa baya.
Mu ƙara dubawa za mu ga hatta a kan Bashar Al’Asad akwai muradu na daban na yammacin duniya da ksar Rasha. Yayin da yammacin duniya ke marawa ’yan gwagwarmaya da ke ganin Asad na uzura mu su, ita kuma Rasha na kare gwamnatin Asad ne. Hakika in ba tare da goyon bayan Hezbollah, Iran da shigowar Rasha ba, da zuwa yau ba a maganar mulkin Bashar Al’Asad. Abubuwan da ke faruwa a yankin gabar ta tsakiya na buƙatar gano muradun dukkan ƙasashen yankin da akasarin su Larabawa ne inda a ke da Isra’ila da Iran da ke kasar Yahudawa da Farisawa.
Kowace ƙasar Larabawa na da irin dangin mutanen ta da abun da su ka sa a gaba a rayuwa. Hatta a Falasɗinu din akwai rarrabuwar kawunna mai yawa tsakanin Hamas da bangaren gwamnatin birnin Ramallah ta Mahmud Abbas. Wani jami’in gwamnatin Ramallah ma na cewa bayan kammala yakin Gaza za a tsame hannun Hamas daga dukkan lamuran mulki don tamkar ƙungiyar ta jawowa Falasɗinawa masifa ne kawai.
Lebanon kuma duk da Larabawa ne amma akwai musulmi da mabiya addinin kirista a cikin su da ke kallon duniya da tabarau daban-daban. Ga Masar kuma da ke da Larabawa masu akidar Boko da kuma ‘yan ƙungiyar IKWAN mabiya marigayi Hasanul Banna. Saudiyya na da malamai mabiya sunnah a gefe guda sai kuma gwamnatin mulkin mulukiyya ta Muhammad bin Sa’ud. Duk bangarorin biyu na da muradu da ke da bambanci da juna a boye ko a bayyane. Mu shiga Yaman inda ’yan tawayen Houthi da ke zama ’yan Shi’a na Zaidiyya da su ka kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnati su ka naɗa kan su a matsayin jagorin ƙasar daga babban birnin ƙasar San’a’a inda ita kuma gwamnatin da a ka zaɓa ta yi gudun hijira zuwa birnin Aden na kudanci. Yau in an ce Houthi na yaƙi da Isra’ila to hakan ba ya nuna ta nag a-maciji da gwamnatin birnin Aden ba ne.
Wasu kuma ƙasashen irin Katar Jodan da Daular Larabawa na fifita wayewar zamani a matsayin mafita ga ɗan adam fiye da batun addini ko Larabci duk da kuma su ɗin ma na mulkin mulukiyya ne. Iraki kuma tun ture gwamnatin marigayi Saddam Hussein kasar ke cikin gallafiri da rashin tabbas. Kuwai kuma da irin Bahrain na kadaran-kadahan. Duk wanda ke tunanin Larabawa za su hada kai su dau matsaya daya bai fahimci siyasar duniya ba sam.
Shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce harin da ƙasar sa ta kai da makamai masu linzami kan Isra’ila daidai ne.
Har zuwa yanzu ba cikakkun bayanan irin barna ko akasin hakan da harin ya haddasa ba kan musamman birnin Tel’aɓiɓ na Isra’ila.
Bayanai daga Isra’ila na baiyana kakkaɓo yawancin makaman da su ka haura 100 da Iran ta harba amma hotunan talabijin na nuna wasu sun dira.
Khamenei a jawabin da ya gabatar yayin jagorantar sallar Jumma’a a Tehran ya ce ƙungiyoyin da ke biyaiya ga Iran ɗin wato kamar Hezbollah da Houthi ba za su kyale Isra’ila ta cigaba da abun da ta ga dama ba taka ma ta birki ba.
Shugaban Amurka Joe Biden ya nuna takaicin harin Iran kan Isra’ila inda ya ce cikin ramuwar da Isra’ila za ta yi har da kan cibiyoyin man fetur na Iran.
Hukumomi a Sham sun ba da alabarin wani hari da Isra’ila ta kai babban birnin ƙasar Damaskas da ya yi sanadiyyar mutuwar farar hula 7.
Bayanai sun nuna Isra’ila ta kai harin ne kan wani gini da zaratan sojojin Iran da ‘yan Hezbollah ke amfani da shi.
Yankin da a ka kai harin na ƙunshe ne da ofisoshin jakadanci da sauran lamuran na diflomasiyya.
Fararen hular da su ka rasa ran su a harin sun haɗa da mata da kananan yara kuma har yanzu ba a gama tantance yawan mutanen da su ka mutu.
Jami’an ceto na cigaba da duba sassan rugujejjen ginin don gano ko akwai masu rai da kuma yiwuwar samun karin waɗanda su ka mutu.
Harin ga hawa 3 na farko na benen ya yi tsanani inda kuma kazalika gine-ginen su ka rufto kan aƙalla motoci 20.
Yaƙi ya rincaɓe tsakanin Isra’ila da Hezbollah:
Yaƙi ya rincabe tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah da Iran ke marawa baya a Lebanon.
Yayin da Iran ke kai hare-hare da makamai masu linzami kan kudancin babban birnin Lebanon Beirut, ita kuma Hezbollah na harba makamai masu linzami da ke shafar garin Haifa a cikin Isra’ila.
Cigaban fitinar ya kawo cikas ga kiraye-kirayen dakatar da mummunan yaƙin da ke lakume rayukan jama’a.
Zuwa yanzu da fara wannan arangamar, fiye da mutum 2000 Lebanawa su ka rasa ran su, a ka ruguza wajen gidaje 50,000 inda wasu dubban mutanen su ka samu raunuka.
Isra’ila ta ce ta kashe jagoran tsare-tsare na Hezbollah a harin da ta kai musamman don halaka shi a kudancin Beirut.
Kazalika Isra’ila ta ce an kashe sojojin ta 30.
Bayanai na nuna Hezbollah na samun galaba a yaƙin klƙasa kan Isra’ila fiye da yadda Isra’ila kan yi amfani da jiragen sama wajen rugurguza gine-gine. Hezbollah na kwantan ɓauna don ƙalubalantar sojojin Isra’ila da ke neman mamaye dukkan yankin kudancin Lebanon. Isra’ila tuntuni ta shawarci mazauna wasu garuruwan kudancin Lebanon su tashi don shirin hare-hare da zummar karya lagon Hezbollah. Duk yanda Isra’ila za ta yi amfani da jiragen yaki da na’urori, ta na bukatar shigowa ta kasa don kafa alamun mamayar ta a Lebanon. Idan an bar Isra’ila da irin tsarin ta ma sai ta mamaye yankunan kudancin Lebanon ta mayar da su ƙasar ta kamar yadda ta yi a tuddan Golan. An hango tutar da Isra’ila ta kafa a wajen wata gona a kudancin Lebanon kafin ta janye don hare-haren rokoki daga Hezbollah.
Kammalawa;
Shin yau ne ko gobe Isra’ila za ta mayar ta martanin harin ƙarin ramuwar gaiya kan Iran? Duk masu sharhi na bayyana damuwa kan illar faɗaɗar wannan yaƙi a gabar ta tsakiya don zai laƙume rayukan jama’a ne ba gaira ba dalili. Ya zama mai muhimmanci a takaita wannan yaƙi da samar da maslaha daga wannan kadarko mai hatsari da a ka shiga. Duk da yakin nan dai dam aba mai ƙarewa ba ne zuwa ma shekaru masu yawa nan gaba, amma aƙalla a dakatar da yaƙin nan a iya shekara ɗaya in an huta wasu shekarun a iya shata wata sabuwar dagar.
