Daga GAMBO ISA
Shugaban ƙungiyar Masu Keke-Napep, Alhaji Umaru Barau a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa jaridun Blueprint a Abuja ya yaba da ɗimbin nasarorin da mai girma gwamnan jihar Yobe ya samu da kuma salon jagorancin Chiroman Gujba a fannin noma, tsarin kula da lafiya a duk faɗin jihar da ƙananan hukumomi 17.
Umaru Barau ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni akan himma wajen bunƙasa noma, ƙarfafawa ‘yan ƙasa da masu ƙaramin ƙarfi da kuma mambobin ƙungiyarsa, inda ya buƙaci mambobinsa da su ci gaba da marawa gwamnati baya domin samar da romon dimokuraɗiyya ga jama’a.
Alhaji Umaru Barau, baya ga shirin ƙarfafawa mambobinsa su yi amfani da tsarin manufofin noma na gwamnati.
Shugaban ya shawarci matasa da su zama jakadu nagari, su guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, su kuma saurari nasihar iyayensu a kodayaushe.
Umar, ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni a fannin samar da ingantattun tsarin kiwon lafiya ta hanyar gina cibiyoyin kula da kiwon lafiya da kuma ɗakunan shan magani a ƙananan hukumomi 17 na jihar, inda ya buƙaci mambobinsa da su ci gajiyar shirin inshorar lafiya a jihar.
Umar ya yi amfani da wannan dama wajen jajentawa gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Borno Shehun Borno, Shehu Garbai Elkanami da Jere ƙaramar hukumar Jere a kwanakin baya ya yi kira ga attajirai, ƙungiyar haɗin gwiwa da su tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a Maiduguri da Jere kwanan nan.
Umaru Barau ya yaba da nasarorin da aka samu & kafa hukumar ci gaban arewa maso gabas (NEDC) ya bukaci hukumar da ta yi la’akari da mambobinsa ta hanyar samar da shirin aiki don mambobinta su ci gajiyar su.
Ya buƙaci mambobinsa da su kasance masu bin doka da oda ta hanyar biyan haraji don tallafa wa gwamnati don ƙara ƙaimi ga ci gaban jihar baki ɗaya, kana su kasance masu haƙuri a koyaushe.
