Wike: Gwamnonin Kudu maso Kudu sun yi barazanar ficewa daga ƙungiyar gwamnoni

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnonin yankin Kudu maso Kudu na Nijeriya sun yi barazanar ficewa daga ƙungiyar Gwamnonin Tarayyar Nijeriya (NGF) har ma da ta Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa (NEC) bisa nuna takaicinta dangane da gazawar ƙungiyar ta yi wajen kare muradun ‘ya’yanta, musamman ma Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas daga zargin tozartawar Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan da Fubara ya gada, Nyesom Wike.

Gwamnonin na Kudu maso Kudu sun nuna matuƙar takaicinsu bisa famkama da nuna isa da suke zargin Wike ya na yi wa gwamnonin PDP, har da shi Gwamna Fubara, don haka suke yin kira da katafariyar murya ga Shugaban Bola Ahmed Tinubu walau ko dai ya ja masa kunne, ko kuma ɗungurumgum ya sauke shi daga muƙaminsa, da zummar samarwa shugabancin ƙungiyar tasu ƙima haɗi da wanzar da zaman lafiya a jihar ta Ribas.

Kamar yadda wannan majiyar ta ruwaito, gwamnonin sun nuna gazawar ƙungiyar na nuna halin kulawa da lamuran da suka jiɓanci ‘ya’yanta, musamman ma yadda ake yin wasan kura da Gwamna Fubara, don haka suke ganin gazawar Shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaƙ, da suke zargin da gazawar haɗa kawunan ‘ya’yan ƙungiyar.

Sun kuma zargi Wike da yunƙurin wargaza da kuma rikirkita jihar ta Ribas, da yunƙurin sauke Fubara daga kan kujerar da ta Gwamna, haɗi da yin munanan kalamai wa gwamnonin jam’iyyar PDP, musamman ma Gwamna Fubara da ya mayar da shi gajeruwar danga.

Wannan kafar sadarwa ta ruwaito cewar, gwamnonin na Kudu maso Kudu suna matuƙar buƙatar sanya hannun Shugaba Tinubu cikin wannan lamari, haɗi da yin kira gare shi na ɗaukar tsauraran matakai domin ganin Minista Wike bai cigaba da haddasa ɓaraka wa jam’iyyar PDP ba, da tayar da hankulan al’ummar jihar Ribas ba.

Sun kuma buƙaci yi wa Gwamna Fubara kariya daga dukkan shaguɓe da barazanar kawar da shi daga kan karagar mulki, haɗi da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a wancan shiyya ta Kudu maso Kudu, domin yin hakan, ita ce hanya ta samun walwala da inganta tattalin arziki.

“Muna roƙon Shugaba Tinubu ya kawo ɗauki cikin lamarin, da marawa shugabancin ƙungiyar gwamnonin na jam’iyyar PDP ta hanyar haɗin Kai da mutumta juna”, a cewar wani majiɓancin ɗaya daga cikin gwamnonin, yana mai jaddada kawo ɗaukin gaggawa wa lamarin.”

By ukarofi