Gwamna Lawal ya ƙaddamar da kwamitoci shida domin aiwatar da manufofin ci gaban Jihar Zamfara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da gudanar da ayyukan ofisoshin gwamnati bisa ƙa’idojin ingantaccen shugabanci.

A ranar Alhamis, Gwamna Lawal ya ƙaddamar da kwamitoci guda shida da aka kafa domin aiwatar da manufofin ci gaban jihar a ɗakin majalisar gidan gwamnati da ke Gusau.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa kwamitocin da aka kafa sun haɗa da: Kwamitin raya al’umma, kwamitin yaƙi da Shaye-shaye, Kwamitin dokar ƙasa da filaye, kwamitin tsare-tsaren ci gaban Zamfara.

Sauran kwamitocin sun haɗa da kwamitin hanyoyin ci gaban al’umma da kwamitin bankin duniya kan masu gudun hijira.

Da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa an zaɓi mambobin kwamitocin daga bangarori daban-daban ciki har da majalisar zartarwa ta jiha, sakatarorin dindindin, ƙwararru, masana ilimi, shugabanni masu ƙwarewa da sauran masana.

Ya ce, “Kwamitin raya al’umma zai kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamna, Mani Mallam Mummini Masamar Mudi, inda mai ba wa gwamna shawara kan harkokin ci gaban al’umma zai kasance a matsayin sakataren kwamitin.”

“Manufar wannan kwamiti ita ce tabbatar da tsarin ingantaccen gudanar da ayyukan al’umma wanda zai ƙara ɗorewar ayyukan gwamnati kan ci gaban ɗan Adam. Haka kuma, zai haɗa da kulawa da hukumomin da ke da alaƙa da ci gaban ɗan Adam domin kauce wa matsala a ayyukan.”

Ta wannan kwamiti, gwamnatin za ta tabbatar da amfani da ilimi da ƙwarewar da al’ummarmu suka samu, musamman matasa da mata, domin basu damar cimma cikakken ƙarfinsu a matsayin masu amfani ga al’umma.

Kwamitin na biyu yana da alhakin magance matsalar shaye-shaye da ke ci gaba da yaɗuwa a jihar. Wannan kwamiti zai yi bincike kan irin miyagun ƙwayoyi da ake amfani da su a cikin al’ummominmu, waɗanda ke amfani da su, da kuma irin yawan abin da ya yi ƙamari.

Sannan zai gano dalilan da suka haddasa matsalar da bayar da shawarwarin magance ta. Uwargidan Gwamna, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ita ce za ta jagoranci wannan kwamiti, yayin da daraktan magunguna na ma’aikatar lafiya zai kasance a matsayin sakataren.

Kwamitin da ke gaba zai kammala tsare-tsaren ci gaban Zamfara na shekara goma (2024-2033). Ayyukan wannan kwamiti shi ne tabbatar da cewa kundin da aka gabatar watanni biyu da suka wuce ya dace da tsare-tsaren ƙasa da ajandar sauyin jihar.

Kwamiti kan dokar ƙasa da filaye zai kasance da alhakin bada shawarwari kan gudanar da harkokin mallakar ƙasa da bayar da izinin amfani da wuraren, wanda zai taimaka wajen gudanar da harkokin mallakar filaye a jihar.

Kwamitin bankin duniya kan masu gudun hijira zai jagoranci aiwatar da tsare-tsaren bankin duniya domin tallafawa ‘yan gudun hijira da al’ummomin da ke karɓarsu a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.

By ukarofi