Hajjin 2025: An buƙaci maniyyatan Edo su fara adashin gata da miliyan N8.4

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Edo, ta umurci dukkan maniyyata aikin Hajjin shekarar 2025 da su yi ajiyar farko ta Naira Miliyan 8.4, har zuwa lokacin da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) za ta fitar da sanarwar ƙarshe.

Shugaban hukumar Ibrahim Oyarekhua ne ya bayar da wannan umarni a ranar Lahadin da ta gabata yayin ganawa da manema labarai a Benin.

Ya jaddada buƙatar samun kuɗaɗen ajiya da wuri, yana mai nuni da canjin manufofin Saudiyya na baya-bayan nan da ke buƙatar a biya aƙalla watanni biyu kafin ranar Arafat.

Oyarekhua ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da aka saba sanar da aikin Hajjin karshe na mako biyu zuwa uku kacal kafin cikar wa’adin biyan kuɗin, yin ajiya na gaba zai taimaka wa alhazai wajen shiryawa da kuma kammala biyan kuɗaɗe kafin lokaci.

Oyarekhua ya ce “Hukumar tana wayar da kan al’ummomin Musulmi kan muhimmancin yin ajiya, ko da ba za a iya biyan cikakken N8.4 miliyan da farko ba,” inji Oyarekhua.

Ya kuma ƙara da cewa, a shekarar da ta gabata, dukkan maniyyatan za su samu nasarar karɓar bizarsu kafin tashi daga wannan sabuwar manufa, inda ya ƙarfafa niyyar alhazai da su saka duk wani kuɗi a asusun hukumar domin samun gurbin zuwa aikin hajji.

By ukarofi