Daga HABU DAN SARKI a Jos
Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar ƙwararrun masu maganin gargajiya ta National Association of Traditional Medicine Practitioners (NANTMP) na ƙasa, Dakta Luka Peter Doka, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta kafa musu Majalisar Gudanarwa, wacce za ta riƙa sa’ido wajen kula da ingancin ayyukan da masu maganin gargajiya ke gudanarwa a Nijeriya, ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya ta ƙasa.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana buƙatar hakan ne jim kaɗan bayan wani taron ganawa da wakilan reshen ƙungiyar na ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, a wani yunƙuri na ƙara farfaɗo da ayyukan ƙungiyar a jihar.
Dakta Luka ya yaba da goyon baya da haɗin kan da masu maganin gargajiya a Jihar Filato suka bashi, wanda ya taimaka wajen samun nasarar sa a babban zaɓen da ƙungiyar ta gudanar a matakin ƙasa. Yayin da ya nemi goyon bayan mambobin ƙungiyar wajen kakkaɓe ɓatagari masu yawo suna tallen maganin gargajiya alhalin basu da ilimi da ƙwarewa a kai.
Ya jaddada cewa, a ƙarƙashin mulkinsa zai yi ƙoƙarin kawo canje-canje masu muhimmanci da za su kawo cigaba a harkar maganin gargajiya.
“Manufata ta farko shi ne in tabbatar an kawar da masu ɓata sana’ar maganin gargajiya. Sannan a tabbatar da cewa, maganin nan ya samu karɓuwa kuma an yi shi bisa ƙa’ida. Kuma mu ga yaya gwamnati za ta fitar da kuɗi don samar da asibitocin maganin gargajiya, yadda za a yi amfani da ingantattun itatuwan maganin gargajiya wajen warkar da marasa lafiya.”
Shugaban ƙungiyar na ƙasa wanda kafin zaɓensa shi ne shugaban ƙungiyar na Arewa, ya kuma nemi bayyana muhimmancin masu maganin gargajiya su ɓullo da tsarin amfani da katin duba marar lafiya, wanda zai ƙunshi bayanai game da mai magani adireshinsa da ɓangaren da yake da ƙwarewa. Sannan a riƙa adana bayanan matakan maganin da aka bi wajen jinyar mara lafiya, domin duk wanda zai zo ya sake jinyarsa daga baya zai bibiyi abubuwan da aka yi amfani da su a farkon jinyar.
Daraktan cibiyar ba da maganin gargajiya ta Bello Herbal Centre da ke Jos, kuma ƙwararren masanin tattalin arziki da ke koyarwa a Jami’ar Jihar Bauchi da ke Gaɗau, Dakta Isma’il Bello ya ƙarfafa buƙatar samar da ingantaccen tsari wajen gudanar da jinyar marasa lafiya, tare da buƙatar sassautawa majinyata, masu buƙatar magani, sakamakon halin da ake ciki na ƙuncin tattalin arziki.
Ya ce, da dama masu zuwa jinya a wajen masu maganin gargajiya a wannan lokaci suna zuwa ne don ba za su iya biyan kuɗin magani a asibiti ba. Ya kamata masu magani su zama masu tausayawa ’yan uwansu, domin sana’a ce ta taimako da neman yardar Allah.
