Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin gyaran ilimi a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ganin yadda ake ta samun yawaitar faɗuwar jarabawar kammala karatun sakandare gwamnan Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da kwamitin da zai duba matsalolin da ke tattare da harkan ilimi tare da gano bakin zaren.

Da yake ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnan jihar, sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba faskari ya bayyana dalilin kafa wannan kwamiti da yace ƙalubalen da ake fuskanta a ɓangaren ilimi ya sa aka kafa kwamitin.

Yace gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin domin gina ginshiƙin ilimi mai ɗorewar ga makomar jihar Katsina.

Sakataren gwamnatin ya ƙara da cewa kwamitin zai mayar da hankali wajen ilimin firamare, sakandire da na gaba da sakandare domin gano matsalolin da suke akwai da kawo hanyoyin magance su.

Ya kuma bayyana cewa aikin kwamitin shine yayi cikakken nazari kan halin da ilimin firamare da sakandare suke ciki a jiha da gano matsalolin da ke hana ci gaban tsarin ilimin firamare da na sakandare a jihar .

Haka kuma kwamitin zai kawo hanyoyin magance matsalolin cikin sauƙi da kuma mai ɗorewar da bada shawarar kan yadda za a inganta ilimin gaba da sakandare a jihar .

“Har ila yau, kwamitin zai samar da shawarwari da za su taimaka wajen bunƙasa gaba ɗayan ɓangaren ilimi”Abdullahi faskari yace .

Ya kuma yi kira ga jama’a da yan asalin jihar da su kawo ta su gudummawar wajen samar da mafita ga ƙalubalen da ake fuskanta a harkar ilimi a jihar ta hanyar bayyana gaban kwamitin ko miƙa takardan shawarwari.

Shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Falalu Bawale shine shugaban kwamitin sai sakatare a ma’aikatar ilimin firamare da sakandare a matsayin sakataren kwamitin.

Sauran mambobin sun haɗa da kwamishinan ilimin firamare da sakandare da mai ba gwamna shawara akan harkokin da suka shafi ilimi.

By ukarofi