Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A Nijeriya, ana cigaba da alhinin rasuwar Babban Hafsan Sojojin ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya kwashe tsawon shekaru yana hidimta wa ƙasar.
Da safiyar Laraba ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da rasuwar Janar Lagbaja bayan ya sha fama da rashin lafiya a ƙasar waje.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan Lagbaja da kuma rundunar sojojin Nijeriya. Ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa da rahama tare da yabawa da muhimmin gudunmawar da ya bayar wa ƙasa.
Kazalika Shugaba Tinubu ya umarci a ɗage zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya saboda nuna alhini da girmama mutuwar Lagbaja.
Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan dabarun yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Ya ce, “An ɗage taron majalisar ne da aka shirya yi yau domin girmama Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojojin ƙasa wanda ya rasu a daren Talata.”
Janar Lagbaja ya yi aiki a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa tun ranar 19 ga Yuni, 2023, har zuwa rasuwarsa a ranar 5 ga Nuwamba, 2024.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin sassauto da tutoci zuwa ƙasa a duk faɗin ƙasa na tsawon kwana bakwai, domin girmama marigayin.
Lagbaja mutum ne mai kishin ƙasa – Buhari:
Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar Babban Hafsan Sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, inda ya bayyana shi a matsayin ɗan kishin ƙasa kuma fitaccen jami’in da ya yi wa ƙasa hidima da ƙwazo.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar bayan sanarwar rasuwar babban hafsan sojin ƙasar, tsohon shugaban ƙasar ya ce ya kaɗu matuƙa da labarin rasuwar, inda ya ƙara da cewa al’ummar ƙasar sun yi rashin ɗaya daga cikin mafi hazaƙan sojoji.
Ya ce, “Lokacin da nake Babban Kwamanda, Lagbaja, a matsayina na ɗaya daga cikin kwamandojin sojoji, ya ɗauki hankalina a matsayin ɗaya daga cikin jajirtattun hafsoshin da suka yi wa ƙasa hidima da ƙwazo.
“A sahun gaba daban-daban na ayyukan tsaron cikin gida da suka haɗa da Operation Zaki a jihar Benue, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu maso Gabashin Nijeriya, da kuma Operation Forest Sanity da ke faɗin jihohin Kaduna da Neja, Janar Lagbaja bai bar kowa a cikin kokwanto ba game da ƙarfin soja.
“Ya bar bayan da ba za a iya mantawa da shi ba a matsayinsa na ƙwararren soja kuma kwamanda mai jan hankali a duk inda ya yi hidima.
Janar Babangida ya miƙa saƙon ta’aziyya:
Tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida GCFR ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban ƙasa kuma kwamandan rundunar sojojin tarayyar Nijeriya Sanata Bola Ahmed Tinubu bisa rasuwar babban hafsan sojojin Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya sanya wa hannu, ta ce rasuwarsa, musamman a wannan lokaci na rayuwarsa da aikinsa, ba kawai babban rashi ne ga iyalansa ba, har ma da ƙasarmu baki ɗaya. Ya kasance babban jami’i kuma jajirtaccen jagoran namiji wanda ke da kishin ƙasa kuma abin koyi.
Babangida ya ƙara da cewa, “Kwarin da ya yi a fagen yaƙi na kawo ƙarshen ta’addanci da tayar da ƙayar baya ya riga ya haifar da sakamako mai kyau, kuma abin takaici ne cewa ba zai kasance a kusa ba don ganin an shawo kan lamarin.”
“A yayin da rundunar sojojin Nijeriya ke ci gaba da yin sadaukarwa domin kare dimokuraɗiyyar mu, da yankin mu, da kare lafiyarmu, ya bi sahun sauran ‘yan ƙasar wajen yaba irin jajircewar da suka nuna,” in ji sanarwar.
Uwargidan Tinubu da Shettima sun ziyarci iyalan Lagbaja:
Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Babban Hafsan Sojin ƙasan Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya rasu.
Ta samu rakiyar matar Mataimakin Shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima, da matar Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro, Hajiya Ribadu.
Sun samu tarba mai kyau daga Uwargidan Shugaban Tsaron ƙasa, Misis Oghogho Musa.
Sanata Tinubu ta yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin, ta kuma rarrashi matar marigayin, Misis Mariya Abiodun Lagbaja.
“Allah ne kaɗai ya san lokacin mutuwar mutum,” in ji uwargidan Tinubu.
A cewar mai ba ta shawara kan harkokin yaɗa labarai, Busola Kukoyi, Uwargidan Shugaban ƙasa ta buƙaci iyalan mamacin da su ɗauki dangana.
Ta kuma ce gwamnati da al’ummar ƙasar nan ba za su manta da irin gudunmawar da Lagbaja ya bayar.
Ma’aikatar Tsaro ta isar ta’aziyyarta:
Ma’aikatar tsaro ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ta miƙa ta’aziyyar rasuwar Laftanar Janar Lagbaja ga iyalansa, Shugaba Tinubu da al’ummar Nijeriya. Badaru ya bayyana Lagbaja a matsayin “jajirtaccen soja mai kishin ƙasa.”
Ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalansa da ‘yan uwa haƙurin rashi.
