An yi asarar biliyoyin Naira sanadiyyar lalacewar lantarki a Kano – Gwamna Yusuf

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Kano ta yi takaicin katsewar hasken wutar lantarki da aka samu a Arewacin Nijeriya a baya-bayan nan, inda ta ce an yi hasarar biliyoyin Naira a jihar ta Kano.

Gwamnatin jihar ƙara da ta damu da yadda ake yawan samun katsewar wutar lantarki a sassa masu muhimmanci da suka haɗa da cibiyoyin kiwon lafiya, cibiyoyin ilimi, da cibiyoyin hada-hadar kuɗi tare da gurgunta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu a ziyarar ban girma da ya kai gidan gwamnati da ke Kano.

Gwamnan ya koka da katsewar wutar lantarki sakamakon munanan ayyuka da ɓarayi ke yi kan muhimman ababen more rayuwa na ƙasa da ke hanyar layin Shiroro zuwa Mando mai ƙarfin 330kɓ, wanda ya taƙaita rayuwar mutane da dama.

Yusuf ya jaddada cewa, tasirin rashin wutar lantarkin ya yi ɓarna sosai a Kano saboda nisa da ta ke da shi zuwa babban layin lantarki, ya ƙara da cewa daman can wutar lantarkin bai isan jihar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya roƙi Ministan da ya tabbatar da cewa Kano ta samu ƙarin Megawatts na lantarki, domin yaba wa kasafin kuɗin da aka ware domin magance matsalar ƙarancin lantarki a jihar.

Hakazalika, Yusuf ya roƙi gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan layin lantarkin Kaduna na biyu – Kano 330Kɓ da Daura-Jogana-Kura 330Kɓ, sannan a gaggauta fara aikin samar da lantarki mai amfani da hasken rana da shugaban ƙasa ya amince da shi ga jihohin Arewa 19.

Ya cewarsa, “katsewar lantarkin ya haifar da gagarumin asarar biliyoyin Naira ga masana’antu a jihar. Hakanan ya shafi ɓangarorin samar da kuɗaɗen shiga, fannin kiwon lafiya da ayyukan yau da kullum na jama’a.”

Gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen ganawa da maziyarcin kan gagarumin ci gaba da aka yi a kan kamfanonin samar da wutar lantarki mai zaman kanta na jihar, wanda aka ƙera domin tara buƙatun wutar lantarki a jihar.

A cewarsa, “ya ​​bayyana cewa tashar samar da wutar lantarki ta Tiga mai ƙarfin megawatts 10 a halin yanzu tana aiki, yayin da na Challawa mai arfin megawatt shida ya kai kashi 65 cikin dari na kammala aikin. Yana da kyau a ambaci cewa gwamnatin jihar tana kan matakin ƙarshe na daidaita duk wani biyan diyya na aikin isar da sako da kamfanin sadarwa na Nijeriya (TCN) ya yi a jihar.”

By ukarofi