Kada mafi girma kuma mafi tsufa a duniya ya mutu

Spread the love

Cassius, kadan da ke rayuwa a ruwa mai gishiri wanda ya riƙe kambun tarihi na Guinness a matsayin kada mafi girma da aka taɓa kamawa, ya mutu a Ostiraliya yana da shekaru sama da 110 a duniya.

Katafaren namun daji mai tsawon mita 5.48 (ƙafa 18), mai nauyin ton ɗaya ya kasance a wurin ajiyar namun daji da ke tsibirin Green Island, kusa da cibiyar yawon buɗe ido na Cairns a ƙueensland.

Sama da shekaru 37, Cassius ya zauna a Marineland Melanesia Crocodile Habitat, inda ya zama dabba mafi kyauna ga mutane, inda ake masa duk abin da ya dace.

A cikin wani saƙon Facebook na baya-bayan nan, cibiyar ajiyar namun dajin ta bayyana cewa Cassius yana fama da rashin lafiya tun ranar 15 ga Oktoba.

Cibiyar ta yaɗa hotonsa yana cin abinci bayan shekarunsa sun ja, Tana mai cewa, “Ya tsufa sosai kuma an yi imanin cewa zai iya rayuwa fiye da na kadar daji.”

An ceto Cassius ne daga wani daji a yankin Arewacin Ostiraliya, inda kadoji ke zama a wani muhimmin sashi na wurin yawon shaƙatawa na yankin.

Cassius ya riƙe kundin tarihin Guinness na duniya na kada mafi girma a duniya a zaman talala. Abin mamaki ne irin yadda wannan halitta ta wuce takwarorinta na daji shekaru a duniya.

By ukarofi