An kama farfesa na yunƙurin rubuta wa ɗiyarsa jarrabawar JAMB

Spread the love

Wata Kotun Majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja, ta ɗaure Jide Josiah Jisos, wanda ya yi ikirarin cewa shi ‘Farfesa’ ne, a gidan yari na tsawon watanni shida, bisa samunsa da laifin yunƙurin rubuta wa ’yarsa jarrabawar UTME na shekarar 2019.

Jami’an hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ne suka kama wanda ake tuhumar a lokacin da yake sa ido akan jarrabawar UTME a makarantar Briɗ Academy da ke Abuja.

Kakakin hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, Jisos ya gabatar da kansa ga jami’an hukumar ta JAMB a matsayin wakilin wata ƙungiya mai zaman kanta, inda ya ce ya zo ne domin sa ido kan jarrabawar. Ba zato ba tsammani, bayan da tawagar da ke sa ido kan jarrabawar ta yi musa tambayoyi, ya kasa bayar da cikakken bayani kan kasancewarsa a wurin.

“Ba a iya tabbatar da ikirarin nasa ba, jami’an tsaro sun kama Jisos don ci gaba da bincike,” in ji sanarwar.

A lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya yarda cewa ba shi da alaƙa da wata ƙungiya mai zaman kanta kuma ya zo ne don ya taimaka wa ɗiyarsa wajen cin jarrabawar UTME.

Alƙalin kotun mai shari’a Folashade Oyekan ta samu Jisos da laifin aikata wani aiki, ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari, tare da zaɓin tarar Naira 100,000.

Sanarwar ba ta fayyace ranar da aka yanke hukuncin ba.

By ukarofi