Wata mata a Abekuta ta cinna wa kanta wuta a makon da ya gabata saboda bashin Naira 70,000 da bankin ƙananan masana’antu ke bin ta.
Matar mai suna Mama Dada ta kona kanta da gidan da ta ke haya ne a unguwar Oke-Keesi da ke ƙaramar Hukumar Abekuta.
Wani ganau mai suna Rasheed Aina ya bayyana wa manema labarai cewa gawar margayiyar ta kone ƙurmus kafin a ciro ta.
“Bashin wani fitaccen bankin masanaantu na yankin ta karɓa har na N70,000 ta kasa biya, shi ne ta kona kanta”, inji shi.
Ya ƙara da cewa,”Wani tsohon ma’aikacin bankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tsarin bankin shi ne duk wanda ya gaza biyan bashin a wani ƙayyadajjen lokaci, tozarci zai biyo baya.
“Ba ƙaramin tozarci nake nufi ba, irin wanda har ’ya’yanka sai sun kasa shiga mutane ne.”
Rahotanni dai na nuna cewa an kai gawar margayiyar ɗakin adana gawa da ke Babban Asibitin Ijaye a jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce basu samu labarin lamarin ba, amma za su gudanar da bincike.
