Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mutane uku ne suka mutu a wani mummunan hatsari da ya rutsa da wata motar siminti ta Dangote.
Hakazalika, haɗarin ya yi sanadinjikkatar wasu da dama a mahaɗar Ayetoro da ke kan hanyar Lekki zuwa Epe a Jihar Legas.
Lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa motar tana saukowa ne daga gadar Ita-Opo a lokacin da motar ta kwace daga hannun direban, kuma ta yi karo da wata mota ƙirar Toyota Camry da ke fake a gefen titi a kasuwar.
Masu ba da agajin gaggawa sun isa wurin don aikim ceto da kuma ba da taimakon gaggawa.
An tura wata motar ɗaukar kaya domin kwashe baraguzan simintin, yayin da hukumomi suka fara samar hanyoyin karkatar da ababen hawa na wucin gadi domin sauƙaƙa cunkoso da kuma tabbatar da lafiyar matafiya.
A halin da ake ciki, hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.
Ta ce, an kai gawarwakin mutanen uku da suka mutu zuwa babban ɗakin ajiye gawa na asibitin Epe.
“An rasa rayuka 3 kuma an kai su ɗakin ajiye gawa a babban asibitin Epe yayin da muke da wata mota ƙirar Tow a ƙasa domin kwashe motocin da abin ya shafa.
Sanarwar ta ce, “An karkatar da ababen hawa don sauƙaƙa zirga-zirga.”
