An kama shugaban ƙwallon ƙafar Afirka ta Kudu

Spread the love

A ranar Laraba ne aka kama shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afirka ta Kudu, Danny Jordaan, bisa zarginsa da yin amfani da kuɗin hukumar domin kansa, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka rawaito.

Sashen binciken manyan laifuka na ƙasar, Hawks, yana duba zargin zamba da almundahana a SAFA tsakanin 2014 zuwa 2018 wanda ya kai dala 72,000.

Ana zargin Jordaan da hayar wani kamfani mai zaman kansa don kare lafiyarsa da kuma kamfanin hulɗa da jama’a ba tare da izini daga hukumar SAFA ba.

Jordaan mai shekaru 73, wanda ya kasance jigo wajen kawo gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2010 zuwa Afrika ta Kudu, ya kasance shugaban SAFA tun shekarar 2013,

An kama shi ne a ranar Laraba kuma ya bayyana a gaban kotun Majistare ta Palm Ridge da ke birnin Johannesburg.

An dai bayar da belin waɗanda ake tuhuma da suka haɗa da babban jami’in kuɗi na SAFA Gronie Hluyo da ɗan kasuwa Treɓor Neethling, waɗanda suka bayyana a kotu tare da Jordaan.

Masu sukar Jordaan dai sun daɗe suna kira gare shi da ya yi murabus, inda suke nuni da gazawar tawagar ƙwallon ƙafa ta maza na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya tun shekara ta 2010 da kuma taɓarɓarewar ababen more rayuwa na ƙwallon ƙafa a ƙasar.

By ukarofi