Gwamna Raɗɗa ya bayar da umarnin ɗaukar matashin da ke tallen ruwa aiki duk da kammala digiri da sakamako mafi daraja

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

A cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga wani ɗalibi, Sham’una na tallar ruwan leda ‘Satchet Water’ a babban birnin tarayya Abuja duk da cewa ɗalibin ya kammala karatunsa na jami’a da sakamako mafi daraja wato ‘First Class’. a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua dake Katsina.

Lamarin ya haifar da cece kuce musamman a shafukan sada zumunta game da matasa dake kammala karatu ba tare da samun aikin yi ba a ƙasar nan.

To sai dai gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya ce ya ga bidiyon ɗalibin don haka ne ya bayar da umarnin ɗaukar Ishaq aikin kai tsaye bayan an gano yana sayar da ruwa domin tallafawa iyayensa.

Bayan ya samu labarin halin da Sham’unu ke ciki, gwamna Raɗɗa ya umarci Mataimakinsa na musamman kan harkokin ɗalibai, Hon. Muhammad Nagaske, da ya bincika gaskiyar bidiyon da ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Binciken ya tabbatar da cewa Sham’unu Ishaq ya kammala karatunsa na digiri na farko a fannin Education/Biology da sakamako mafi kyau a shekarar 2021/2022. Wannan shaida ta samu tabbaci daga Mataimakin Shugaban Jami’ar.

Sham’unu, wanda ya kammala aikin bautar ƙasa (NYSC) a Jihar Taraba, ya shiga sana’ar sayar da ruwa don cike buƙatunsa da na iyalinsa.

“Ya kamata a yaba wa haziƙai ba a bar su cikin wahala ba,” in ji Gwamna Raɗɗa yayin bayar da umarnin tabbatar da ɗaukar Sham’unu aiki ta hannun Shugaban Ma’aikata.

“Gwamnatinmu za ta ci gaba da gano haziƙan matasa da za su taka rawar gani wajen ci gaban jihar Katsina.” Inji shi.

Wannan matakin ya yi daidai da ƙudirin gwamna Raɗɗa na ganin an ɗaukaka harkokin ilimi da kuma ba wa ƙwararrun matasa dama.

A watan da ya gabata ma, ranar 12 ga Oktoba, 2024, Gwamnan ya bayar da aikin kai tsaye ga ɗalibai tara da suka yi fice a Kwalejin Ilimi ta Isah Kaita dake Dutsinma. Haka zalika, a ranar 26 ga Mayu, 2024, gwamnan ya xauki ɗalibai tara da suka yi digiri na farko daga Jami’ar Umaru Musa Yar’adua a bikin kammala karatu na haɗin gwiwa na jami’ar.

“Gwamnatinmu ta fahimci cewa makomar Jihar Katsina tana hannun matasanmu masu hazaka,” in ji Gwamna Raɗɗa.

“Za mu ci gaba da samar da damar da za su ba wa matasa damar amfani da iliminsu da fasaharsu domin amfanin al’umma.”

By ukarofi