Lakurawa: manufofinsu da ayyukansu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kawo yanzu dai ba sabon labari ba ne cewa an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’adda a arewa maso yammacin Nijeriya da ake kira da Lakurawa, kalmar da aka ce ta samo asali ne daga kalmar turancin faranshi na ‘recrue’ wanda ke nufin sabbin ɗauka. Amma sai aka hausantar da kalmar zuwa, Lakurawa. Ko daga sunan za mu fahimci waɗannan ‘yan ta’adda na da alaƙa da yankin ƙasashen rainon Faransa da ke yankin Afirka ta Yamma. Sannan kiransu da kalmar ‘recrue’ shi ma alama ce da ke nuna aikin soja ko wani abu da ya shafi tsaro.

Ga masana harkokin tsaro ko waɗanda ke bibiyar al’amuran da ke faruwa a yankin arewa maso yamma a ƙasar nan, ya san wannan ƙungiya ba baƙuwa ba ce. Sai dai abin da yake baƙo shi ne bayyanar sunanta daga bakin hukumomi, wanda ke nuna alamun lamarin ya fara ƙazancewa. Tunda har Gwamnatin Jihar Kebbi da kanta ta ankarar da hukumomin tsaro da sauran mahukunta, kamar yadda aka san  al’adar ‘yan Nijeriya ba sa tashi farga da abu sai ya fara fin ƙarfinsu.

A nazarin da na yi daga ɓangarori daban-daban, na fahimci cewa, wannan ƙungiya da asalin sunanta shi ne ‘Jama’atu Muslimun’, wato Jama’ar Musulmi, ta jima da bayyana a yankin yammacin Afirka, kuma kamar yadda sunanta ya nuna ƙungiya ce ta mutane masu iƙirarin bin koyarwar addinin Musulunci, da kuma aiki da dokokinsa a rayuwarsu. Kuma tana da mambobi masu yawa daga ƙabilu da ‘yan ƙasashe daban-daban, kama daga Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, Nijeriya, har zuwa Cote de Iɓore wato Kotdibuwa. Don haka ana iya samun kowacce irin ƙabila a cikinta. Farkon abin da aka fara sanin ‘yan ƙungiyar da shi shi ne wa’azi, a kasuwanni da wuraren ibada. Suna kira zuwa ga biyayya ga dokokin shari’ar addinin Musulunci sau da ƙafa. Shugabansu, kamar yadda bayanai suka nuna shi ne Ameer Habib Tajje.

Bayanai sun nuna cewa, Lakurawa mutane ne masu yawo kamar fulanin daji, wato Baroro, basa zama waje ɗaya, kuma suna yawo ne a cikin tawaga a kan babura. Misalin irin hotunan da muke gani na zugar ‘yan bindiga masu kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara. Sannan suna yawo tare da dabbobinsu waɗanda da su ne suke cin abinci ko abin sha. Don haka ake danganta rayuwarsu da ta Fulani, duk kuwa da kasancewar ba zallar Fulani ba ne. Babu wani waje ɗaya da za a ce wannan shi ne sansanin ‘yan ƙungiyar Lakurawa, kamar yadda Dr Mustapha Ahmed Rufa’i na Sashin Nazarin Tarihi a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ya bayyana. Kodayake wasu rahotanni na nuni da cewa ana ganin taruwarsu a dazukan Tsauni da Marake.

Da farko an ce yawansu bai wuce mutum 200 ko kusa da haka ba, amma kawo yanzu sun ninka haka nesa ba kusa ba, kuma yawancinsu matasa ne da ba su wuce shekara 18 zuwa 35 ba. Sai dai harwayau akwai zargin suna cigaba da jan hankalin matasa wajen kwaɗaita musu kuɗi don su bi ra’ayinsu, kodayake zargi ne da bai tabbata ba. Masu nazari kan ƙungiyoyin addini masu ra’ayin jihadi na ganin idan sabuwar aƙida ta bayyana kuɗi bai cika tasiri wajen jan ra’ayin matasa, kamar tunanin sauyin rayuwa da samun tsira a gobe ƙiyama yake saurin jansu ba. Da kuma halin matsin rayuwa da ake fuskanta, bisa kwaɗayin samun abin da za a ci da yadda za a samu rufin asiri.

Jama’a sun fara bayyana damuwa ne daga ayyukan su yayin da su Lakurawa suka fara ƙoƙarin tursasawa jama’a aiki da dokokin shari’a, a duk wuraren da suka shiga. Da kuma tsorata su kan za su hukunta duk wanda ya tona musu asiri ko ya kai bayanansu ga hukumomi. Kamar misalin tilastawa mutane tsayar da gemu, hana shan giya ko sigari, tilastawa mata rufe jiki, da kuma matsantawa masu dukiya fitar da Zakka, musamman dabbobi. An ce daga cikin Zakkar da suke karɓa ne suke amfani da su a matsayin kadara ko abinci. Sannan akwai zarge-zarge da ake yi musu na yin ƙwace daga hannun mutane ba tare da son ransu ba, wato kamar fashi da makami kenan.

Harwayau, akwai batun zargin da ake yi musu na kai wa jami’an tsaro hari da riƙon makamai, inda aka ce suna tanadar manyan makamai na yaƙin ƙasa da ƙasa, har da ƙananan na’urorin da ake harbawa sama don a aika su leƙen asiri a wani waje, wanda hakan babbar barazana ce a sha’anin tsaro. Kodayake wani rahoton jami’an tsaro ya bayyana Lakurawa, a matsayin wata ƙungiyar makiyaya da ke yawo da iyalinsa da dabbobinsu, ba tare da nuna wata alamar barazanar tsaro ba. 

Wasu jama’a a yankin Gudu da Tangaza a cikin Jihar Sakkwato, sun kai kuka ga hukumomi tun shekaru shida da suka gabata cewa waɗannan baƙi fa suna yi musu barazana a harkokinsu na rayuwa, amma babu wani muhimmin mataki da suka ɗauka saboda ana ganin ba su nuna wata shaida da ke nuna fitina ko ta’addanci ba.

Rahotanni sun bayyana cewa ko a kwanakin baya da rikici ya haɗa su da mutanen yankin Mera a ƙaramar Hukumar Augie da ke Jihar Kebbi, wanda har ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15, yana da nasaba ne da yadda su Lakurawan aka ce sun ƙwace dabbobin wani mutum a bayan garin Mera yana kiwo. Shi kuma wannan mutumin ya koma gari ya sanar da jama’a waɗanda su kuma su yi wo gayya suka far wa Lakurawan, da nufin ƙwato dabbobin da aka ƙwace, har abin ya kai ga asarar rayuka.

Wannan na daga cikin abin da ya ƙara tsorata jama’a da ayyukan ‘yan wannan ƙungiya, musamman da aka ce har sun fara sanya doka da haraji ga mazauna wasu ƙananan hukumomi a Jihar Sakkwato, inda har ma ake raɗe-raɗin ƙwace ikon Wasu yankunan a ƙananan Hukumomin Binji, Gudu, Illelah, Tangaza, da Sila me, da wasu ƙauyuka a iyakokin Nijeriya da Nijar, irin su Gwangwano, Mulawa, Wassaniya, da Tunigara. Har ma wasu rahotanni na nuni da cewa, wannan ƙungiya ta sanyawa yankunan da take riƙe da su sunan ‘Darul Islam’, wato ƙasar Musulunci.

Yayin da nake wannan rubutu, rahotanni na bayyana cewa, biyo bayan umarnin shugaban ƙasa Bola Tinubu da Babban Mashawarcin Shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, jami’an tsaro sun kai farmaki kan wuraren da ake zargin Lakurawa na zaune a Jihar Kebbi, har sun fatattake su, tare da ƙwace dabbobin da ake zargin sun ƙwace a wajen mutane. Wannan labari na gaggawar kai ɗauki da jami’an tsaron Nijeriya suka kai kan waɗannan ‘yan ta’adda abin a yaba ne sosai, sai dai kuma fatan hakan zai cigaba a duk sauran sassan jihohin da abin ya shafa, don hana su komawa wani ɓangaren suna cutar da jama’a.

Sannan a cigaba da ƙoƙarin ganin bayan waɓannan ɓata-garin mutane, rundunar tsaro ta ƙasa ta bayar da cigiyar wasu jiga-jigai daga cikinsu, da suka haɗa da Abu Khadijah, Abdurrahman, Dadi Gumba da aka fi sani da Abu Muhammad, Usman Shehu, Abu Yusuf, Musa Wa’a, Ibrahim Suyeka, Ba Sulhu da Idris Taklakse.

Duk da kasancewar shugabannin rundunonin tsaron Nijeriya da haɗin gwiwar takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar, ta bakin ministan tsaron ƙasa, Muhammadu Badaru Abubakar, suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun hana wannan ƙungiya tasiri, ta hanyar ayyukan haɗin gwiwa, da neman goyon bayan shugabannin al’umma da sauran jama’a. Lallai akwai buƙatar a cire siyasa da son zuciya a cikin ayyukan da za a yi, domin kaucewa kuskuren da aka yi na baya lokacin bayyanar ƙungiyar Boko Haram.

Sannan kuma kamar yadda Dr Mustapha Ahmed Rufa’i na Sashin Nazarin Tarihi a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ya bayyana, Lakurawa da Boko Haram ba su kaɗai ne ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu iƙirarin aƙidar jihadi a arewacin Nijeriya ba, ana ganin akwai ƙungiyoyin ta’addanci da yawansu ya kai kimanin 13, irin su ƙungiyar Ansaru, JASS, JASWA, ISWA da sauransu, waɗanda ake tunanin suna da daruruwan mayaƙa a ƙarƙashin su, da kuma makamai iri-iri. Sannan akwai zargin suna da hulɗa da sauran ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da suke dazukan jihohin Kaduna, Neja, Kogi da Kwara. Daga cikinsu ne ma aka gano suke da hannu wajen katsewar wutar lantarki a wasu sassan ƙasar nan, sakamakon buƙatar da suke da ita wajen gwamnati na neman a sako musu wasu mutanen su da ake tsare da su.

Yana da muhimmanci jami’an tsaro su riƙa amfani da bayanai irin waɗannan domin samar da dabaru na yadda za a murƙushe irin waɗannan ‘yanta’adda, domin ƙalubale da barazanar da rayuwar ‘yan Nijeriya ke ciki. A daina bari sai ƙungiya ta fara riƙa ko ta fara zama alaƙaƙai kafin a ce za a ɗauki mataki a kanta, musamman saboda lura da ƙarancin jami’an tsaro da muke fama da su a ƙasar nan.

By ukarofi