Daga HABU DAN SARKI a Jos
Kungiyar Raya Unguwar Abba Na Shehu da ke ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, ta karrama wasu fitattun ‘ya’yan unguwar su 18, waɗanda suka nuna bajinta, kuma suka yi zarra a wasu ɓangarori na rayuwa. Daga cikinsu akwai ma’aikatan gwamnati, ‘yan siyasa, malaman addini da malaman jami’a da kuma ‘yan kasuwa.
A yayin wani babban taro da ƙungiyar ta gudanar a ɗakin taro na Babban Masallacin Jumma’a na Jos, shugaban ƙungiyar, Alhaji Auwal El-Mansoor ya bayyana cewa, an zaɓo waɗannan fitattun mutane ne daga sassa uku na Unguwar Abba Na Shehu, kuma al’ummar unguwar ne suka tantance su kafin a miƙa sunayensu ga ƙungiyar.
A cikinsu, kamar yadda ya ce, akwai waɗanda suka samu sabbin muƙamai a gwamnati, ko a wuraren ayyukansu, da kuma hidimar da suke yi ta al’umma, a ciki ma har wasu bayin Allah biyu da Allah Ya karɓi ransu a lokacin da suke tsakiyar hidimar al’umma.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Babban Sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam, Farfesa Khalid Aliyu Abubakar, da Farfesa Abdulƙadir Suleiman na Jami’ar Abuja, da Farfesa Balarabe Yusha’u na Jami’ar Abubakar Tafawa ɓalewa dake Bauchi, Farfesa Sani Adamu Tal, na Jami’ar Jos, Farfesa Yusuf Abdullahi Yusuf, daga Jami’ar Jos, da kuma Farfesa Dawood Abubakar shi ma daga Jami’ar Jos, waɗanda dukkannin su suka samu matsayin Farfesa ko ƙaramin Farfesa a jami’o’in da suke aiki.
Bayan su akwai waɗanda suka samu muƙamin Dakta a fagen karatu, da suka haɗa da Dr. Abdulhamid A. Abdullahi, Dr. Sani Garba Shehu, da kuma Dr. Bashir Ma’aruf Sani.
Sannan kuma akwai Babban Limamin Jos, Sheikh Ghazali Isma’ila Adam wanda aka naɗa ba da jimawa ba, bayan rasuwar tsohon Babban Limamin Jos wanda Allah Ya yi wa rasuwa.
Daga ɓangaren ‘yan siyasa, an karrama sabon Mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Honarabul Kabiru Muhammad Garkuwa da sabon Kansilan Unguwar Abba Na Shehu, Honarabul Auwal Hassan Tubarkallah, da kuma Honarabul Umar Abubakar ɗanfari.
An kuma karrama, Malam Mukhtar Ibrahim Garaje, da Malama Zainab Mustapha, sakamakon sadaukarwa da jajircewarsu kan hidimar al’umma da cigaban Unguwar Abba Na Shehu. Sai, marigayi Malam Muhammad Isma’il, da marigayi Alhaji Ibrahim Auta, waɗanda Allah Ya yi wa rasuwa, amma kafin rasuwarsu sun hidimtawa wannan ƙungiya da al’ummar unguwar bakiɗaya.
Shugaban taron, Alhaji Ibrahim Saleh Hassan, wanda ya fito daga Unguwar Gangare, ya tunatar da waɗanda aka karrama ɗin su kiyaye haƙƙoƙin da ke kansu na taimakawa al’ummar su da ‘yan unguwar da suka fito. Kuma su cigaba da nuna halayya tagari, don zama jakadun wannan anguwa na ƙwarai. Ya buƙaci mambobin wannan anguwa su riƙa tallafawa junansu, musamman a irin yanayin da ake ciki na ƙuncin tattalin arziki da taɓarɓarewar tarbiyya.
Ya ce, “Babu wanda zai taimaka muku don cigaban ku daga wani waje sai in ku ne ku ka tashi ku ka taimaki kanku da kanku.”
A nasa jawabin, shugaban al’umma kuma Turakin Jos, Alhaji Garba Abdulƙadir, ya yaba da ƙoƙarin da ƙungiyar Abba Na Shehu take yi, tare da jan hankalin mutanen da aka karrama kada su ja baya daga al’ummar su, kuma a duk lokacin da aka nemi gudunmawar su to, su yi abin da ya kamata. Sannan su buɗe ƙofofin su ga jama’ar unguwarsu.
Ya ƙarfafa buƙatar shugabanni su yi abin da ya dace, wajen haɗa kan al’ummarsu da yin aikin da zai kawo wa al’ummarsu cigaba.
Taron ya samu halartar shugabannin ƙananan Hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, da ɓokkos, waɗanda suka marawa ɗan uwansu Honarabul Kabiru Garkuwa baya, a matsayinsa na sabon Mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, saboda kyakkyawar alaƙar da yake da ita da abokansa na siyasa da na unguwa.
