Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Karamin Kwamitin Lafiya na Kwamitin ba da tallafi na musamman na Gidauniyar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato ya kammala zagayen ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato 23 da nufin tantance ɗaliban da ke karatu a makarantun nazarin kiwon lafiya da ke faɗin Jihar Sakkwato.
Shugaban ƙaramin kwamitin, Malam Kabiru Shehu Binji shi ya bayyana hakan jim kaɗan da kammala zagayen wanda aka yi a cibiyoyi 6 da ke jihar, da suka haɗa da Cibiyar Yaɗa Addinin Musulunci ta IET da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Sakkwato ta Arewa, Sakkwato ta Kudu, Wamakko, Dange Shuni, Tureta, Boɗinga, da Rabah. Yayin da Cibiyar Goronyo ta ƙunshi cibiyoyin ƙananan hukumomin Goronyo, Isa, Wurno, da Sabon Birni.
Cibiyar Tangaza da ke Gidan Madi kuwa ta ƙunshi ƙananan hukumomin Tangaza, Silame, Binji, Gudu, da Kware. Yayin da cibiyar yankin Tambuwal take da ƙananan hukumomin Tambuwal, Kebbe, Yabo, da Shagari, sai kuma gundumomin da ke ƙananan hukumomin Gwadabawa, Illela, da Gada a cibiyar Gwadabawa.
A dukkan cibiyoyin nan an gudanar da tantancewar cikin nasara, bayan da kwamitin mutum huɗu na ƙananan hukumomin suka zaƙulo ɗalibai goma-goma don rubutawa da fitar da zakaru mutun huɗu. Malam Aminu Bello Gwadabawa, Alh Isa Mai’alewa daga Goronyo da Gwadabawa sun bayyana cewa sun zaƙulo ɗaliban ne bisa ga amanar da aka basu. Sannan an gudanar da jarabawar ne a darussan Lissafi da kuma Turanci. Yayin da wasu daga cikin ɗaliban da suka shiga aikin tantancewar sun yi godiya da fatan samun nasara.
Malam Kabiru ya yi godiya ga babban kwamitin ƙarƙashin Malam Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato da suka ba su damar gudanar da aikin, inda ya yaba wa Gwamnatin Jihar Sakkwato akan hidimar da takewa addinin Musulunci da al’umma bakiɗaya.
Shugabannin ƙananan hukumomin Goronyo da Gwadabawa da Wakilin Ubanƙasar Tambuwal, duk sun yi godiya ga Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Attahiru Bafarawa akan wannan aikin alheri da yake gudanarwa.
Kwamitin mai mutun 7 wanda ya ƙunshi wakilan Nana Girls, ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya Musulmi ta IMAN, da sauransu, ya gudanar da tantancewar ne a tsawon mako guda.
