Daga USMAN KAROFI
Sabuwar ƙungiya ta ta’addanci mai suna Lukarawa ta kafa sansaninta a ƙananan hukumomi 10 a jihohin Sokoto da Kebbi kafin a gano ayyukanta kimanin makonni uku da suka gabata. Rahotanni sun nuna cewa mambobin ƙungiyar sun fara kafa sansaninsu a wasu ƙauyuka da ke kan iyaka tsakanin Nijeriya da Nijar, da suka haɗa da Gwanaguano, Mulawa, Wassinya, da Turigaic.
Daga bisani sun tsallaka Nijeriya inda suka kafa sansaninsu a wasu yankuna, musamman a ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza a jihar Sokoto tun a shekarar 2018. Wasu daga cikin shugabannin ƙungiyar sun haɗa da Abu Khadijah, Abdulrahman (Idi), Dadi Gumba, Muhammad Abu, Usman Shehu, Abu Yusuf, Musa Walia, Ibrahim Suyaka, Ba Sulhu da Idris Taklakse. A cewar majiyoyi suna amfani da harshen Hausa, Fulfulde, da Larabci wajen wa’azinsu, sannan suna kiran sansaninsu da sunan Darul Islam.
Wani daga cikin shugabannin yankin a ƙaramar hukumar Tangaza ya bayyana cewa yawancin mambobin ƙungiyar suna da shekaru tsakanin 18 zuwa 50, inda suka saba kai farmaki kan ƙauyuka don karɓar haraji daga jama’a ba tare da kashe kowa ba, har zuwa harin da suka kai a kwanan nan a garin Mera. Ya ce su kan ƙirga dabbobin da suke a hannun jama’a kuma su fitar da kashi daga ciki a matsayin haraji wanda suke ƙarba daga dabbobin.
Dr. Murtala Rufa’i, wani masani daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, ya bayyana cewa ƙungiyar ta shafe fiye da shekaru 25 tana shirin kafa daular ta, tare da kafa sansaninsu a wurare daban-daban a ƙananan hukumomi kimanin 10 da suka haɗa da Sokoto da Kebbi. Ya ce suna yawan canza wurin zama daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar amfani da babura, wanda ke sanya wa jami’an tsaro wahalar samun su, sai dai idan hanyarsu ta yi karo da su.
A cewar Rufa’i, an kore su daga wasu yankuna tare da taimakon jami’an tsaro a shekarar 2020, amma sun sake dawowa a watan Disambar 2023. Ya ƙara da cewa, tun bayan dawowarsu ayyukansu sun bazu zuwa ƙananan hukumomi 10 da suka haɗa da Tangaza, Gudu, Illela, Gwadabawa, Kware, Silame da Binji a jihar Sokoto da kuma Augie, Kangiwa, da Argungu a jihar Kebbi. Rufa’i ya bayyana cewa ƙungiyar asalin ta kasance wata ƙungiya ce daga ƙasar Mali mai suna Jama’atu Muslimina da ke cikin yankin Sahel.
Ƙungiyar tana jawo wasu daga cikin matasa na yankunan da take aiki da su ta hanyar basu kuɗaɗe, kayan noma, da na’urar ban ruwa. Wani daga cikin mazauna garin Gongono a ƙaramar hukumar Tangaza, wanda ya bayyana kansa da suna Mainasara, ya tabbatar da kasancewar ƙungiyar a yankin. Ya bayyana cewa, kwanan nan ƙungiyar ta kama wani matashi daga ƙauyen su wanda suka zarga da alaƙa da jami’an tsaro kuma daga bisani suka kashe shi.
